Abubakar Mahmoud Gumi
Shafi 176 na Mushaf yana ɗauke da ayoyi 11. Yana cikin Juz 9, Hizb 18.
An sabunta a 10 Yuli 2026 03h52
coran.read_full_page : Kara Shafi 176 na Alkur'ani →
إِنَّ وَلِـِّۧىَ ٱللَّهُ ٱلَّذِى نَزَّلَ ٱلْكِتَـٰبَ ۖ وَهُوَ يَتَوَلَّى ٱلصَّـٰلِحِينَ ﴿١٩٦﴾
"Lalle ne, Majiɓincĩna Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi kuma Shĩ ne Yake jiɓintar sãlihai,"
وَٱلَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَسْتَطِيعُونَ نَصْرَكُمْ وَلَآ أَنفُسَهُمْ يَنصُرُونَ ﴿١٩٧﴾
"Kuma waɗanda kuke kira, baicinSa, bã su iya taimakõn ku, kuma kansu ma, bã su iya taimaka."
وَإِن تَدْعُوهُمْ إِلَى ٱلْهُدَىٰ لَا يَسْمَعُوا۟ ۖ وَتَرَىٰهُمْ يَنظُرُونَ إِلَيْكَ وَهُمْ لَا يُبْصِرُونَ ﴿١٩٨﴾
Kuma idan ka kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su ji ba, kuma kanã ganin su, sunã dũbi zuwa gare ka, alhãli kuwa sũ, bã su gani.
خُذِ ٱلْعَفْوَ وَأْمُرْ بِٱلْعُرْفِ وَأَعْرِضْ عَنِ ٱلْجَـٰهِلِينَ ﴿١٩٩﴾
Ka riƙi abin da ya sauƙaƙa; Kuma ka yi umurni da alhẽri, Kuma ka kau da kai daga jãhilai.
وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ ٱلشَّيْطَـٰنِ نَزْغٌۭ فَٱسْتَعِذْ بِٱللَّهِ ۚ إِنَّهُۥ سَمِيعٌ عَلِيمٌ ﴿٢٠٠﴾
Kuma imma wata fizga daga Shaiɗan ta fizge ka, sai ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai jĩ ne, Masani.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوْا۟ إِذَا مَسَّهُمْ طَـٰٓئِفٌۭ مِّنَ ٱلشَّيْطَـٰنِ تَذَكَّرُوا۟ فَإِذَا هُم مُّبْصِرُونَ ﴿٢٠١﴾
Lalle ne waɗanda suka yi taƙawa idan wani tãshin hankali daga Shaiɗan ya shãfe su, sai su tuna (Allah) sai gã su, sun zama masu basĩra.
وَإِخْوَٰنُهُمْ يَمُدُّونَهُمْ فِى ٱلْغَىِّ ثُمَّ لَا يُقْصِرُونَ ﴿٢٠٢﴾
Kuma 'yan'uwan su (shaiɗanu) sunã taimakon su a cikin ɓata, sa'an nan kuma bã su taƙaitãwa.
وَإِذَا لَمْ تَأْتِهِم بِـَٔايَةٍۢ قَالُوا۟ لَوْلَا ٱجْتَبَيْتَهَا ۚ قُلْ إِنَّمَآ أَتَّبِعُ مَا يُوحَىٰٓ إِلَىَّ مِن رَّبِّى ۚ هَـٰذَا بَصَآئِرُ مِن رَّبِّكُمْ وَهُدًۭى وَرَحْمَةٌۭ لِّقَوْمٍۢ يُؤْمِنُونَ ﴿٢٠٣﴾
Kuma idan ba ka je musu da wata ãyã ba, su ce: "Don me ba ka ƙãga ta ba?" Ka ce: "Abin sani kawai, inã biyar abin da aka yõ wahayi zuwa gare ni ne, daga Ubangjina. Wannan abũbuwan kula ne daga Ubangijinku, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin imãni."
وَإِذَا قُرِئَ ٱلْقُرْءَانُ فَٱسْتَمِعُوا۟ لَهُۥ وَأَنصِتُوا۟ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ ﴿٢٠٤﴾
Kuma idan an karanta Alƙur'ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama.
وَٱذْكُر رَّبَّكَ فِى نَفْسِكَ تَضَرُّعًۭا وَخِيفَةًۭ وَدُونَ ٱلْجَهْرِ مِنَ ٱلْقَوْلِ بِٱلْغُدُوِّ وَٱلْـَٔاصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ ٱلْغَـٰفِلِينَ ﴿٢٠٥﴾
Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsõro, kuma kõmabãyan bayyanawa na magana, da sãfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu.
إِنَّ ٱلَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ لَا يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِهِۦ وَيُسَبِّحُونَهُۥ وَلَهُۥ يَسْجُدُونَ ۩ ﴿٢٠٦﴾
Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka bã su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sunã tsarake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada.