Abubakar Mahmoud Gumi
Shafi 220 na Mushaf yana ɗauke da ayoyi 9. Yana cikin Juz 11, Hizb 22.
An sabunta a 10 Yuli 2026 03h52
coran.read_full_page : Kara Shafi 220 na Alkur'ani →
فَلَوْلَا كَانَتْ قَرْيَةٌ ءَامَنَتْ فَنَفَعَهَآ إِيمَـٰنُهَآ إِلَّا قَوْمَ يُونُسَ لَمَّآ ءَامَنُوا۟ كَشَفْنَا عَنْهُمْ عَذَابَ ٱلْخِزْىِ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَمَتَّعْنَـٰهُمْ إِلَىٰ حِينٍۢ ﴿٩٨﴾
To, dõmin me wata alƙarya ba ta kasance ta yi ĩmãniba har ĩmãninta ya amfãne ta, fãcemutãnen Yũnus? A lõkacin da suka yi ĩmãni, Munjanye azãbar wulãkanci daga gare su a cikin rãyuwar dũniya. Kuma Muka jiyar da su dãɗi zuwa wani lõkaci.
وَلَوْ شَآءَ رَبُّكَ لَـَٔامَنَ مَن فِى ٱلْأَرْضِ كُلُّهُمْ جَمِيعًا ۚ أَفَأَنتَ تُكْرِهُ ٱلنَّاسَ حَتَّىٰ يَكُونُوا۟ مُؤْمِنِينَ ﴿٩٩﴾
Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã waɗanda suke a cikin ƙasa sun yi ĩmãni dukansu gabã ɗaya. Shin, kai kanã tĩlasta mutãnene har su kasance mãsu ĩmãni?
وَمَا كَانَ لِنَفْسٍ أَن تُؤْمِنَ إِلَّا بِإِذْنِ ٱللَّهِ ۚ وَيَجْعَلُ ٱلرِّجْسَ عَلَى ٱلَّذِينَ لَا يَعْقِلُونَ ﴿١٠٠﴾
Kuma ba ya kasancẽwa ga wani rai ya yi ĩmãni fãce da iznin Allah, kuma (Allah) Yanã sanya ƙazanta a kan waɗanda bã su yin hankali.
قُلِ ٱنظُرُوا۟ مَاذَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَمَا تُغْنِى ٱلْـَٔايَـٰتُ وَٱلنُّذُرُ عَن قَوْمٍۢ لَّا يُؤْمِنُونَ ﴿١٠١﴾
Ka ce: "Ku dũbi abin da yake cikin sammai da ƙasa."Kuma ãyõyi da gargaɗi bã su wadãtarwa ga mutãne waɗanda bã su yin ĩmãni.
فَهَلْ يَنتَظِرُونَ إِلَّا مِثْلَ أَيَّامِ ٱلَّذِينَ خَلَوْا۟ مِن قَبْلِهِمْ ۚ قُلْ فَٱنتَظِرُوٓا۟ إِنِّى مَعَكُم مِّنَ ٱلْمُنتَظِرِينَ ﴿١٠٢﴾
To, Shin sunã jiran wani abu fãce kamar misãlin kwãnukan waɗanda suka shũɗe daga gabãninsu? Ka ce: "Ku yi jira! Lalle nĩ tãre da ku, inã daga mãsu jira."
ثُمَّ نُنَجِّى رُسُلَنَا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ۚ كَذَٰلِكَ حَقًّا عَلَيْنَا نُنجِ ٱلْمُؤْمِنِينَ ﴿١٠٣﴾
Sa'an nan kuma Munã kuɓutar da manzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, kamar wannan ne, tabbatacce ne a gare Mu, Mu kuɓutar da mãsu ĩmãni.
قُلْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِن كُنتُمْ فِى شَكٍّۢ مِّن دِينِى فَلَآ أَعْبُدُ ٱلَّذِينَ تَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَـٰكِنْ أَعْبُدُ ٱللَّهَ ٱلَّذِى يَتَوَفَّىٰكُمْ ۖ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ ﴿١٠٤﴾
Ka ce: "Yã kũ mutãne! Idan kun kasance a cikin kõkanto daga addinĩna, to bã ni bauta wa, waɗanda kuke, bautã wa, baicin Allah, kuma amma ina bauta wa Allah wanda Yake karɓar rãyukanku. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu ĩmãni."
وَأَنْ أَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفًۭا وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ ﴿١٠٥﴾
"Kuma (an ce mini): Ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã karkatl zuwa ga gaskiya, kuma kada ka kasance daga mãsu shirka.
وَلَا تَدْعُ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَ ۖ فَإِن فَعَلْتَ فَإِنَّكَ إِذًۭا مِّنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ ﴿١٠٦﴾
"Kuma kada ka kirãyi, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin ka kuma bã ya cũtar ka. To, idan ka aikata haka, sa'an nan lalle kai, a lõkacin, kanã daga mãsu zãlunci."