Kara Ruku'u 142 na Alkur'ani

Ruku'u 142 daga Surah Al-Araf ne (ayoyi 163 zuwa 171). Yana ɗauke da ayoyi 9 kuma yana cikin Juz 9.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Ruku 142 a cikin Alkur'ani

9
ayoyi
1
Surah
9
Juz
v.163 – v.171
Ayoyi

Surori a cikin Ruku 142

الأعراف · Juz 9
Shafi 171
Ruku'u 142
سورة الأعراف
Juz 9 47.2% (75/159)
Hizb 17 90.4% (75/83)

وَسْـَٔلْهُمْ عَنِ ٱلْقَرْيَةِ ٱلَّتِى كَانَتْ حَاضِرَةَ ٱلْبَحْرِ إِذْ يَعْدُونَ فِى ٱلسَّبْتِ إِذْ تَأْتِيهِمْ حِيتَانُهُمْ يَوْمَ سَبْتِهِمْ شُرَّعًۭا وَيَوْمَ لَا يَسْبِتُونَ ۙ لَا تَأْتِيهِمْ ۚ كَذَٰلِكَ نَبْلُوهُم بِمَا كَانُوا۟ يَفْسُقُونَ ﴿١٦٣﴾

Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga tẽku, a lõkacin da suke ƙẽtare haddi a cikin Asabar, a lõkacin da kĩfãyensu, suke je musu a rãnar Asabar ɗinsu jẽre. Kuma a rãnar da ba su yi Asabar ba, bã su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.

وَإِذْ قَالَتْ أُمَّةٌۭ مِّنْهُمْ لِمَ تَعِظُونَ قَوْمًا ۙ ٱللَّهُ مُهْلِكُهُمْ أَوْ مُعَذِّبُهُمْ عَذَابًۭا شَدِيدًۭا ۖ قَالُوا۟ مَعْذِرَةً إِلَىٰ رَبِّكُمْ وَلَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ ﴿١٦٤﴾

Kuma a lõkacin da wata al'umma daga gare su ta ce: "Don me kuke yin wa'azi ga mutãne waɗanda Allah Yake Mai halaka su kõ kuwa Mai yi musu azãba, azãba mai tsanani?" Suka ce: "Dõmin nẽman hanzari zuwa ga Ubangijinku, kuma tsammãninsu, sunã yin taƙawa."

فَلَمَّا نَسُوا۟ مَا ذُكِّرُوا۟ بِهِۦٓ أَنجَيْنَا ٱلَّذِينَ يَنْهَوْنَ عَنِ ٱلسُّوٓءِ وَأَخَذْنَا ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ بِعَذَابٍۭ بَـِٔيسٍۭ بِمَا كَانُوا۟ يَفْسُقُونَ ﴿١٦٥﴾

To, a lõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, Mun tsĩrar da waɗanda suke hani daga cũta, kuma Muka kãma waɗanda suka yi zãlunci, da azãba mai tsanani dõmin abin da suka kasance sunã yi, na fasiƙanci.

فَلَمَّا عَتَوْا۟ عَن مَّا نُهُوا۟ عَنْهُ قُلْنَا لَهُمْ كُونُوا۟ قِرَدَةً خَـٰسِـِٔينَ ﴿١٦٦﴾

Sa'an nan a lõkacin da suka yi girman kai daga barin abin da aka hana su daga gare shi, Muka ce musu: "Ku kasance birai ƙasƙantattu."

وَإِذْ تَأَذَّنَ رَبُّكَ لَيَبْعَثَنَّ عَلَيْهِمْ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ مَن يَسُومُهُمْ سُوٓءَ ٱلْعَذَابِ ۗ إِنَّ رَبَّكَ لَسَرِيعُ ٱلْعِقَابِ ۖ وَإِنَّهُۥ لَغَفُورٌۭ رَّحِيمٌۭ ﴿١٦٧﴾

Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, lalle ne, zã Ya aika a kansu (Yahũd), zuwa, Rãnar¡iyãma, wanda zai ɗanɗana musu mummunar azãba, lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai gaggawar uƙũba ne, kuma shĩ haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

وَقَطَّعْنَـٰهُمْ فِى ٱلْأَرْضِ أُمَمًۭا ۖ مِّنْهُمُ ٱلصَّـٰلِحُونَ وَمِنْهُمْ دُونَ ذَٰلِكَ ۖ وَبَلَوْنَـٰهُم بِٱلْحَسَنَـٰتِ وَٱلسَّيِّـَٔاتِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ ﴿١٦٨﴾

Kuma Muka yayyanka su, a cikin ƙasa, al'ummõmi, daga gare su akwai sãlihai, kuma daga gare su akwai wanda bã haka ba. Muka jarrabe su da abũbuwan alhẽri da na musĩfa; Tsammãninsu, sunã kõmõwa.

فَخَلَفَ مِنۢ بَعْدِهِمْ خَلْفٌۭ وَرِثُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ يَأْخُذُونَ عَرَضَ هَـٰذَا ٱلْأَدْنَىٰ وَيَقُولُونَ سَيُغْفَرُ لَنَا وَإِن يَأْتِهِمْ عَرَضٌۭ مِّثْلُهُۥ يَأْخُذُوهُ ۚ أَلَمْ يُؤْخَذْ عَلَيْهِم مِّيثَـٰقُ ٱلْكِتَـٰبِ أَن لَّا يَقُولُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلْحَقَّ وَدَرَسُوا۟ مَا فِيهِ ۗ وَٱلدَّارُ ٱلْـَٔاخِرَةُ خَيْرٌۭ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ ﴿١٦٩﴾

Sai wasu' yan bãya suka maye daga bãyansu, sun gaji Littãfin, sunã karɓar sifar wannan ƙasƙantacciya, sunã cẽwa: "Zã a gãfarta mana. "Iadan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karɓe ta. Shin, ba a karɓi alkawarin Littãfi ba a kansu cẽwa kada su faɗa ga Allah, fãce gaskiya, alhãli kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma Gidan Lãhira ne mafi alhẽriga wanda ya yi taƙawa? Shin, bã zã ku hankalta ba?

وَٱلَّذِينَ يُمَسِّكُونَ بِٱلْكِتَـٰبِ وَأَقَامُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجْرَ ٱلْمُصْلِحِينَ ﴿١٧٠﴾

Kuma waɗanda suke riƙẽwa da laittãfi kuma suka tsayar da salla, lalle ne Mũ, bã Mu tõzarta lãdar mãsu gyãrãwa.

۞ وَإِذْ نَتَقْنَا ٱلْجَبَلَ فَوْقَهُمْ كَأَنَّهُۥ ظُلَّةٌۭ وَظَنُّوٓا۟ أَنَّهُۥ وَاقِعٌۢ بِهِمْ خُذُوا۟ مَآ ءَاتَيْنَـٰكُم بِقُوَّةٍۢ وَٱذْكُرُوا۟ مَا فِيهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ ﴿١٧١﴾

Kuma a lõkacin da muka ɗaukaka dũtse sama da su, kumar dai shi girgije ne, kuma suka haƙƙaƙe, lalle ne shĩ, mai fãɗuwa ne a gare su, (aka ce): "Ku karɓi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammãninku kunã yin taƙawa."

بسم الله الرحمن الرحيم Lit 10 Rabi' al-Awwal
الاثنين 10 ربيع الأول
أحدب متزايد Cikakken Wata Tasowa Rana 11.3 / 29.5
Haske 87%
Cikakken Wata a cikin kwana 3
سبحان الله وبحمده Tsarkin Allah da godiyarSa