Kara Ruku'u 226 na Alkur'ani

Ruku'u 226 daga Surah An-Nahl ne (ayoyi 22 zuwa 25). Yana ɗauke da ayoyi 4 kuma yana cikin Juz 14.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Ruku 226 a cikin Alkur'ani

4
ayoyi
1
Surah
14
Juz
v.22 – v.25
Ayoyi

Surori a cikin Ruku 226

النحل · Juz 14
Kewaya
Alamomi
Sauti
Hadda
Nuni
Shafi 269
◄ Ruku'u 226 ►
سورة النحل
Juz 14 52.9% (120/227)
Hizb 27 80.5% (120/149)

إِلَـٰهُكُمْ إِلَـٰهٌۭ وَٰحِدٌۭ ۚ فَٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ قُلُوبُهُم مُّنكِرَةٌۭ وَهُم مُّسْتَكْبِرُونَ ﴿22﴾

Abin bautawarku, abin bautãwa ne guda, to, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, zukãtansu mãsu musu ne, kuma su makangara ne.

لَا جَرَمَ أَنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ ۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلْمُسْتَكْبِرِينَ ﴿23﴾

Haƙĩƙa, lalle ne, Allah Yanã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa. Lalle ne Shi, bã Ya Son mãsu girman kai.

وَإِذَا قِيلَ لَهُم مَّاذَآ أَنزَلَ رَبُّكُمْ ۙ قَالُوٓا۟ أَسَـٰطِيرُ ٱلْأَوَّلِينَ ﴿24﴾

Idan aka ce musu: "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Sai su ce: "Tãtsũniyõyin mutãnen farko."

لِيَحْمِلُوٓا۟ أَوْزَارَهُمْ كَامِلَةًۭ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۙ وَمِنْ أَوْزَارِ ٱلَّذِينَ يُضِلُّونَهُم بِغَيْرِ عِلْمٍ ۗ أَلَا سَآءَ مَا يَزِرُونَ ﴿25﴾

Dõmin su ɗauki zunubansu cikakku a Rãnar ¡iyãma, kuma daga zunuban waɗanda suke ɓatarwa bã da wani ilmi ba. To, abin da suke ɗauka na zunubi ya mũnana.

بسم الله الرحمن الرحيم Alh 25 Rabi' al-Thani
الخميس 25 ربيع الآخر
هلال متناقص Gajimaren Raguwa Rana 27.1 / 29.5
Haske 7%
Wata Sabo a cikin kwana 2
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah