Ruku'u 265 daga Surah Maryam ne (ayoyi 16 zuwa 40). Yana ɗauke da ayoyi 25 kuma yana cikin Juz 16.
An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34
Karanta duka cikakken : Kara Ruku'u 265 na Alkur'ani →
وَٱذْكُرْ فِى ٱلْكِتَـٰبِ مَرْيَمَ إِذِ ٱنتَبَذَتْ مِنْ أَهْلِهَا مَكَانًۭا شَرْقِيًّۭا ﴿١٦﴾
Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas.
فَٱتَّخَذَتْ مِن دُونِهِمْ حِجَابًۭا فَأَرْسَلْنَآ إِلَيْهَا رُوحَنَا فَتَمَثَّلَ لَهَا بَشَرًۭا سَوِيًّۭا ﴿١٧﴾
Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci.
قَالَتْ إِنِّىٓ أَعُوذُ بِٱلرَّحْمَـٰنِ مِنكَ إِن كُنتَ تَقِيًّۭا ﴿١٨﴾
Ta ce: "Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!"
قَالَ إِنَّمَآ أَنَا۠ رَسُولُ رَبِّكِ لِأَهَبَ لَكِ غُلَـٰمًۭا زَكِيًّۭا ﴿١٩﴾
Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki."
قَالَتْ أَنَّىٰ يَكُونُ لِى غُلَـٰمٌۭ وَلَمْ يَمْسَسْنِى بَشَرٌۭ وَلَمْ أَكُ بَغِيًّۭا ﴿٢٠﴾
Ta ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?"
قَالَ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ هُوَ عَلَىَّ هَيِّنٌۭ ۖ وَلِنَجْعَلَهُۥٓ ءَايَةًۭ لِّلنَّاسِ وَرَحْمَةًۭ مِّنَّا ۚ وَكَانَ أَمْرًۭا مَّقْضِيًّۭا ﴿٢١﴾
Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce."
۞ فَحَمَلَتْهُ فَٱنتَبَذَتْ بِهِۦ مَكَانًۭا قَصِيًّۭا ﴿٢٢﴾
Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa.
فَأَجَآءَهَا ٱلْمَخَاضُ إِلَىٰ جِذْعِ ٱلنَّخْلَةِ قَالَتْ يَـٰلَيْتَنِى مِتُّ قَبْلَ هَـٰذَا وَكُنتُ نَسْيًۭا مَّنسِيًّۭا ﴿٢٣﴾
Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!"
فَنَادَىٰهَا مِن تَحْتِهَآ أَلَّا تَحْزَنِى قَدْ جَعَلَ رَبُّكِ تَحْتَكِ سَرِيًّۭا ﴿٢٤﴾
Sai (yãron da ta haifa) ya kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki.
وَهُزِّىٓ إِلَيْكِ بِجِذْعِ ٱلنَّخْلَةِ تُسَـٰقِطْ عَلَيْكِ رُطَبًۭا جَنِيًّۭا ﴿٢٥﴾
"Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu."
فَكُلِى وَٱشْرَبِى وَقَرِّى عَيْنًۭا ۖ فَإِمَّا تَرَيِنَّ مِنَ ٱلْبَشَرِ أَحَدًۭا فَقُولِىٓ إِنِّى نَذَرْتُ لِلرَّحْمَـٰنِ صَوْمًۭا فَلَنْ أُكَلِّمَ ٱلْيَوْمَ إِنسِيًّۭا ﴿٢٦﴾
"Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba."
فَأَتَتْ بِهِۦ قَوْمَهَا تَحْمِلُهُۥ ۖ قَالُوا۟ يَـٰمَرْيَمُ لَقَدْ جِئْتِ شَيْـًۭٔا فَرِيًّۭا ﴿٢٧﴾
Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma!
يَـٰٓأُخْتَ هَـٰرُونَ مَا كَانَ أَبُوكِ ٱمْرَأَ سَوْءٍۢ وَمَا كَانَتْ أُمُّكِ بَغِيًّۭا ﴿٢٨﴾
"Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba."
فَأَشَارَتْ إِلَيْهِ ۖ قَالُوا۟ كَيْفَ نُكَلِّمُ مَن كَانَ فِى ٱلْمَهْدِ صَبِيًّۭا ﴿٢٩﴾
Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?"
قَالَ إِنِّى عَبْدُ ٱللَّهِ ءَاتَىٰنِىَ ٱلْكِتَـٰبَ وَجَعَلَنِى نَبِيًّۭا ﴿٣٠﴾
Ya ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi."
وَجَعَلَنِى مُبَارَكًا أَيْنَ مَا كُنتُ وَأَوْصَـٰنِى بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ مَا دُمْتُ حَيًّۭا ﴿٣١﴾
"Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai."
وَبَرًّۢا بِوَٰلِدَتِى وَلَمْ يَجْعَلْنِى جَبَّارًۭا شَقِيًّۭا ﴿٣٢﴾
"Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri."
وَٱلسَّلَـٰمُ عَلَىَّ يَوْمَ وُلِدتُّ وَيَوْمَ أَمُوتُ وَيَوْمَ أُبْعَثُ حَيًّۭا ﴿٣٣﴾
"Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai."
ذَٰلِكَ عِيسَى ٱبْنُ مَرْيَمَ ۚ قَوْلَ ٱلْحَقِّ ٱلَّذِى فِيهِ يَمْتَرُونَ ﴿٣٤﴾
Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta.
مَا كَانَ لِلَّهِ أَن يَتَّخِذَ مِن وَلَدٍۢ ۖ سُبْحَـٰنَهُۥٓ ۚ إِذَا قَضَىٰٓ أَمْرًۭا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ ﴿٣٥﴾
Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa.
وَإِنَّ ٱللَّهَ رَبِّى وَرَبُّكُمْ فَٱعْبُدُوهُ ۚ هَـٰذَا صِرَٰطٌۭ مُّسْتَقِيمٌۭ ﴿٣٦﴾
"Kuma lalle Allah ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici."
فَٱخْتَلَفَ ٱلْأَحْزَابُ مِنۢ بَيْنِهِمْ ۖ فَوَيْلٌۭ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِن مَّشْهَدِ يَوْمٍ عَظِيمٍ ﴿٣٧﴾
Sai ƙungiyõyin suka sãɓã wa jũna a tsakãninsu. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma.
أَسْمِعْ بِهِمْ وَأَبْصِرْ يَوْمَ يَأْتُونَنَا ۖ لَـٰكِنِ ٱلظَّـٰلِمُونَ ٱلْيَوْمَ فِى ضَلَـٰلٍۢ مُّبِينٍۢ ﴿٣٨﴾
Mẽne ne ya yi jinsu, kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin ɓata bayyananna.
وَأَنذِرْهُمْ يَوْمَ ٱلْحَسْرَةِ إِذْ قُضِىَ ٱلْأَمْرُ وَهُمْ فِى غَفْلَةٍۢ وَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ ﴿٣٩﴾
Kuma ka yi musu gargaɗi da rãnar nadãma a lõkacin da aka hukunta al'amari alhãli kuwa sunã a cikin ɓãta, kuma sũ bã su yin ĩmãni.
إِنَّا نَحْنُ نَرِثُ ٱلْأَرْضَ وَمَنْ عَلَيْهَا وَإِلَيْنَا يُرْجَعُونَ ﴿٤٠﴾
Lalle ne Mũ, Mũ ne ke gãdon ƙasa da wanda yake a kanta, kuma zuwa gare Mu ake mayar da su.