Kara Ruku'u 284 na Alkur'ani

Ruku'u 284 daga Surah Al-Anbiya ne (ayoyi 94 zuwa 112). Yana ɗauke da ayoyi 19 kuma yana cikin Juz 17.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Ruku 284 a cikin Alkur'ani

19
ayoyi
1
Surah
17
Juz
v.94 – v.112
Ayoyi
الأنبياء · Juz 17
Kewaya
Alamomi
Sauti
Hadda
Nuni
Shafi 330
◄ Ruku'u 284 ►
سورة الأنبياء
Juz 17 48.9% (93/190)
Hizb 33 83.0% (93/112)

فَمَن يَعْمَلْ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ وَهُوَ مُؤْمِنٌۭ فَلَا كُفْرَانَ لِسَعْيِهِۦ وَإِنَّا لَهُۥ كَـٰتِبُونَ ﴿94﴾

Dõmin wanda ya aikata daga ayyukan kwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bãbu musu ga aikinsa, kuma Mu Mãsu rubũtãwa gare shi ne.

وَحَرَٰمٌ عَلَىٰ قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَـٰهَآ أَنَّهُمْ لَا يَرْجِعُونَ ﴿95﴾

Kuma hananne ne a kan wata alƙarya da Muka halakar cẽwa lalle sũ, bã su kõmõwa.

حَتَّىٰٓ إِذَا فُتِحَتْ يَأْجُوجُ وَمَأْجُوجُ وَهُم مِّن كُلِّ حَدَبٍۢ يَنسِلُونَ ﴿96﴾

Har sa'ad da aka bũde Yãjũju da Mãjũju alhãli kuwa sunã gaggãwa daga kõwane tudun ƙasa.

وَٱقْتَرَبَ ٱلْوَعْدُ ٱلْحَقُّ فَإِذَا هِىَ شَـٰخِصَةٌ أَبْصَـٰرُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ يَـٰوَيْلَنَا قَدْ كُنَّا فِى غَفْلَةٍۢ مِّنْ هَـٰذَا بَلْ كُنَّا ظَـٰلِمِينَ ﴿97﴾

Kuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, (sunã cẽwa), "Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! Ã'a, mun kasance dai mãsu zãlunci!"

إِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنتُمْ لَهَا وَٰرِدُونَ ﴿98﴾

(A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne."

لَوْ كَانَ هَـٰٓؤُلَآءِ ءَالِهَةًۭ مَّا وَرَدُوهَا ۖ وَكُلٌّۭ فِيهَا خَـٰلِدُونَ ﴿99﴾

Dã waɗannan (abũbuwanbautãwar) sun kasance abũbuwan bautãwar gaskiya ne, dã ba su tusga mata ba, alhãli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne.

لَهُمْ فِيهَا زَفِيرٌۭ وَهُمْ فِيهَا لَا يَسْمَعُونَ ﴿100﴾

Sunã da wata hargõwa a cikinta, alhãli kuwa sũ, a cikinta, bã su saurãren kõme.

إِنَّ ٱلَّذِينَ سَبَقَتْ لَهُم مِّنَّا ٱلْحُسْنَىٰٓ أُو۟لَـٰٓئِكَ عَنْهَا مُبْعَدُونَ ﴿101﴾

Lalle ne waɗanda kalmar yabo tã gabãta a garẽ su daga garẽ Mu, waɗannan waɗanda ake nĩsantarwa daga barinta ne.

لَا يَسْمَعُونَ حَسِيسَهَا ۖ وَهُمْ فِى مَا ٱشْتَهَتْ أَنفُسُهُمْ خَـٰلِدُونَ ﴿102﴾

Bã su jin sautin mõtsinta alhãli kuwa sũ madawwamãne a cikin abin da rãyukansu suka yi marmarinsa.

لَا يَحْزُنُهُمُ ٱلْفَزَعُ ٱلْأَكْبَرُ وَتَتَلَقَّىٰهُمُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ هَـٰذَا يَوْمُكُمُ ٱلَّذِى كُنتُمْ تُوعَدُونَ ﴿103﴾

Firgitar nan mafi girma, bã zã ta baƙantã musu rai ba. Kuma malã'iku na yi musu marãba (sunã cẽwa) "Wannan yininku nẽ wanda kuka kasance anã yi muku wa'adi da shi."

يَوْمَ نَطْوِى ٱلسَّمَآءَ كَطَىِّ ٱلسِّجِلِّ لِلْكُتُبِ ۚ كَمَا بَدَأْنَآ أَوَّلَ خَلْقٍۢ نُّعِيدُهُۥ ۚ وَعْدًا عَلَيْنَآ ۚ إِنَّا كُنَّا فَـٰعِلِينَ ﴿104﴾

A rãnar da Muke naɗe sãma kamar neɗẽwar takarda ga abũbuwan rubũtãwa kamar yadda Muka fãra a farKon halitta Muke mãyar da ita. Wa'adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa.

وَلَقَدْ كَتَبْنَا فِى ٱلزَّبُورِ مِنۢ بَعْدِ ٱلذِّكْرِ أَنَّ ٱلْأَرْضَ يَرِثُهَا عِبَادِىَ ٱلصَّـٰلِحُونَ ﴿105﴾

Kuma lalle haƙĩƙa Mun rubũta a cikin Littãfi baicin Ambato (Lauhul Mahfũz) cẽwa ƙasã, bayĩNa sãlihai, sunã gãdonta.

إِنَّ فِى هَـٰذَا لَبَلَـٰغًۭا لِّقَوْمٍ عَـٰبِدِينَ ﴿106﴾

Lalle ne a cikin wannan (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, akwai iyarwa (ga maganar da ta gabãta ga waɗansu mutãne mãsu ibãda.

وَمَآ أَرْسَلْنَـٰكَ إِلَّا رَحْمَةًۭ لِّلْعَـٰلَمِينَ ﴿107﴾

Kuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai.

قُلْ إِنَّمَا يُوحَىٰٓ إِلَىَّ أَنَّمَآ إِلَـٰهُكُمْ إِلَـٰهٌۭ وَٰحِدٌۭ ۖ فَهَلْ أَنتُم مُّسْلِمُونَ ﴿108﴾

Ka ce: "Abin sani kawai, anã yin wahayi zuwa gare ni ne, cẽwa, lalle ne, Abin bautãwarku, Abin bautãwa ne Guda. To shin kũ mãsu mĩƙa wuya ne?"

فَإِن تَوَلَّوْا۟ فَقُلْ ءَاذَنتُكُمْ عَلَىٰ سَوَآءٍۢ ۖ وَإِنْ أَدْرِىٓ أَقَرِيبٌ أَم بَعِيدٌۭ مَّا تُوعَدُونَ ﴿109﴾

Sa'an nan idan suka jũya, to, ka ce: "Nã sanar da ku, a kan daidaita, kuma ban sani ba, shin, abin da ake yi muku wa'adi makusanci ne Kõ kuwa manĩsanci?"

إِنَّهُۥ يَعْلَمُ ٱلْجَهْرَ مِنَ ٱلْقَوْلِ وَيَعْلَمُ مَا تَكْتُمُونَ ﴿110﴾

"Lalle ne Shĩ (Allah) Yanã sanin bayyane daga magana, kuma Yanã sanin abin da kuke ɓõyẽwa.

وَإِنْ أَدْرِى لَعَلَّهُۥ فِتْنَةٌۭ لَّكُمْ وَمَتَـٰعٌ إِلَىٰ حِينٍۢ ﴿111﴾

"Kuma ban sani ba, tsammãninsa ya zama fitina a gare ku, kõ kuma don jin dãɗi, zuwa ga wani ɗan lõkaci."

قَـٰلَ رَبِّ ٱحْكُم بِٱلْحَقِّ ۗ وَرَبُّنَا ٱلرَّحْمَـٰنُ ٱلْمُسْتَعَانُ عَلَىٰ مَا تَصِفُونَ ﴿112﴾

Ya ce: "Yã Ubangiji! Ka yi hukunci da gaskiya. Kuma Ubangijinmu Mai rahama ne Wanda ake nẽman taimakonSa a kan abinda kuke siffantãwa."

بسم الله الرحمن الرحيم Asa 27 Rabi' al-Thani
السبت 27 ربيع الآخر
هلال متناقص Gajimaren Raguwa Rana 28.3 / 29.5
Haske 2%
Wata Sabo a cikin kwana 1
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah