Kara Ruku'u 329 na Alkur'ani

Ruku'u 329 daga Surah An-Naml ne (ayoyi 32 zuwa 44). Yana ɗauke da ayoyi 13 kuma yana cikin Juz 19.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Ruku 329 a cikin Alkur'ani

13
ayoyi
1
Surah
19
Juz
v.32 – v.44
Ayoyi

Surori a cikin Ruku 329

النمل · Juz 19
Shafi 379
Ruku'u 329
سورة النمل
Juz 19 92.9% (315/339)
Hizb 38 86.0% (148/172)

قَالَتْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْمَلَؤُا۟ أَفْتُونِى فِىٓ أَمْرِى مَا كُنتُ قَاطِعَةً أَمْرًا حَتَّىٰ تَشْهَدُونِ ﴿٣٢﴾

Ta ce: "Yã ku mashawarta! Ku yi Mini fatawa ga al'amarĩna, ban kasance mai yanke wani al'amari ba, sai kun halarta."

قَالُوا۟ نَحْنُ أُو۟لُوا۟ قُوَّةٍۢ وَأُو۟لُوا۟ بَأْسٍۢ شَدِيدٍۢ وَٱلْأَمْرُ إِلَيْكِ فَٱنظُرِى مَاذَا تَأْمُرِينَ ﴿٣٣﴾

Suka ce: "Mũ ma'abũta ƙarfi ne, kuma ma'abbũta yãƙi mai tsanani ne, kuma al'amari yã kõma zuwa gare ki, sabõda haka ki dũbamẽne ne zã ki yi umurui (da shi)?"

قَالَتْ إِنَّ ٱلْمُلُوكَ إِذَا دَخَلُوا۟ قَرْيَةً أَفْسَدُوهَا وَجَعَلُوٓا۟ أَعِزَّةَ أَهْلِهَآ أَذِلَّةًۭ ۖ وَكَذَٰلِكَ يَفْعَلُونَ ﴿٣٤﴾

Ta ce: "Lalle sarakuna idan sun shiga wata alƙarya, sai su ɓãta ta, kuma su sanya mãsu darajar mutãnenta ƙasƙantattu. Kuma kamar wancan ne suke likatãwa."

وَإِنِّى مُرْسِلَةٌ إِلَيْهِم بِهَدِيَّةٍۢ فَنَاظِرَةٌۢ بِمَ يَرْجِعُ ٱلْمُرْسَلُونَ ﴿٣٥﴾

"Kuma lalle nĩ mai aikãwa ce zuwa gare su da kyauta, sa'an nan mai dũbawa ce: Da me manzannin zã su kõmo."

فَلَمَّا جَآءَ سُلَيْمَـٰنَ قَالَ أَتُمِدُّونَنِ بِمَالٍۢ فَمَآ ءَاتَىٰنِۦَ ٱللَّهُ خَيْرٌۭ مِّمَّآ ءَاتَىٰكُم بَلْ أَنتُم بِهَدِيَّتِكُمْ تَفْرَحُونَ ﴿٣٦﴾

To, a lõkacin da ya jẽ wa Sulaiman ya ce: "Shin, za ku ƙãra ni da dũkiya ne? To, abin daAllah Ya bã ni, shi ne mafi alhẽridaga abin da Ya bã ku. A'a, kũ nekuke yin farin ciki da kyautarku."

ٱرْجِعْ إِلَيْهِمْ فَلَنَأْتِيَنَّهُم بِجُنُودٍۢ لَّا قِبَلَ لَهُم بِهَا وَلَنُخْرِجَنَّهُم مِّنْهَآ أَذِلَّةًۭ وَهُمْ صَـٰغِرُونَ ﴿٣٧﴾

"Ka kõma zuwa gare su. Sa'an nan lalle munã je musu da rundunõni, bãbu wata tãɓukawa gare su game da su, kuma lalle munã fitar da su daga gare ta, sunã mafi wulãkantuwa, kuma sunã ƙasƙantattu."

قَالَ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْمَلَؤُا۟ أَيُّكُمْ يَأْتِينِى بِعَرْشِهَا قَبْلَ أَن يَأْتُونِى مُسْلِمِينَ ﴿٣٨﴾

Ya ce: "Yã ku mashãwarta! Wannenku zai zo mini da gadonta a gabãnin su zo, sunã mãsu sallamãwa?"

قَالَ عِفْرِيتٌۭ مِّنَ ٱلْجِنِّ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبْلَ أَن تَقُومَ مِن مَّقَامِكَ ۖ وَإِنِّى عَلَيْهِ لَقَوِىٌّ أَمِينٌۭ ﴿٣٩﴾

Wani mai ƙarfi daga aljannu ya ce: "Nĩ inã zo maka da shi a gabãnin ka tãshi daga matsayinka. Kuma llale nĩ a gare shi, haƙĩƙa, mai ƙarfi ne amintacce."

قَالَ ٱلَّذِى عِندَهُۥ عِلْمٌۭ مِّنَ ٱلْكِتَـٰبِ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبْلَ أَن يَرْتَدَّ إِلَيْكَ طَرْفُكَ ۚ فَلَمَّا رَءَاهُ مُسْتَقِرًّا عِندَهُۥ قَالَ هَـٰذَا مِن فَضْلِ رَبِّى لِيَبْلُوَنِىٓ ءَأَشْكُرُ أَمْ أَكْفُرُ ۖ وَمَن شَكَرَ فَإِنَّمَا يَشْكُرُ لِنَفْسِهِۦ ۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّى غَنِىٌّۭ كَرِيمٌۭ ﴿٤٠﴾

Wanda yake a wurinsa akwai wani ilmi daga Littafin ya ce: "Ni inã zo maka da shi a gabãnin ƙyaftãwar ganinka ta kõma gare ka." To, a lõkacin da ya gan shi matabbaci a wurinsa, ya ce: "Wannan daga falalar Ubangijĩna yake, dõmin Ya jarraba ni: Shin, zan gõde ne, kõ kuwa zan butulce! Kuma wanda ya gõde, to, yanã gõdẽwa ne dõmin kansa, kuma wanda ya kãfirta, to, lalle Ubangijina Wadãtacce ne, Karĩmi."

قَالَ نَكِّرُوا۟ لَهَا عَرْشَهَا نَنظُرْ أَتَهْتَدِىٓ أَمْ تَكُونُ مِنَ ٱلَّذِينَ لَا يَهْتَدُونَ ﴿٤١﴾

Ya ce: "Ku canza kamar gadonta gare ta, mu gani, shin zã ta shiryu, kõ kuwa tanã kasancẽwa daga waɗanda bã su shiryuwa."

فَلَمَّا جَآءَتْ قِيلَ أَهَـٰكَذَا عَرْشُكِ ۖ قَالَتْ كَأَنَّهُۥ هُوَ ۚ وَأُوتِينَا ٱلْعِلْمَ مِن قَبْلِهَا وَكُنَّا مُسْلِمِينَ ﴿٤٢﴾

To a lõkacin da ta jẽ aka ce "Shin, kamar wannan gadon sarautarki yake?" Ta ce: "Kamar dai shĩne. Kuma an bã mu ilmi daga gabãninta kuma mun kasance mãsu sallamãwar (al'amari ga Allah)."

وَصَدَّهَا مَا كَانَت تَّعْبُدُ مِن دُونِ ٱللَّهِ ۖ إِنَّهَا كَانَتْ مِن قَوْمٍۢ كَـٰفِرِينَ ﴿٤٣﴾

Kuma abin da ta kasance tanã bautãwa, baicin Allah, ya kange ta. Lalle ita, tã kasance daga mutãne kãfirai.

قِيلَ لَهَا ٱدْخُلِى ٱلصَّرْحَ ۖ فَلَمَّا رَأَتْهُ حَسِبَتْهُ لُجَّةًۭ وَكَشَفَتْ عَن سَاقَيْهَا ۚ قَالَ إِنَّهُۥ صَرْحٌۭ مُّمَرَّدٌۭ مِّن قَوَارِيرَ ۗ قَالَتْ رَبِّ إِنِّى ظَلَمْتُ نَفْسِى وَأَسْلَمْتُ مَعَ سُلَيْمَـٰنَ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ ﴿٤٤﴾

Aka ce mata, "Ki shiga a gidan sarauta." To, a lõkacin da ta gan shi, ta yi zatona wai gurbi ne, kuma ta kuranye daga ƙwaurinta. Ya ce: "Lalle ne shi, gidan sarauta ne mai santsi daga madũbai." Ta ce: "Yã Ubangijĩna! Bã a rõƙon Allah sai da sunãyensa mãsu kyau, tis'in da taran nan, sai dai a dunƙule kamar a ce, "Inã rõƙon Allah da sunãyenSa da na sani da waɗanda ban sani ba." Lalle nĩ, na zãlunci kaina, kuma nã sallama al'amari tãre da Sulaiman ga Allah, Ubangijin halittu."

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 11 Rabi' al-Awwal
الثلاثاء 11 ربيع الأول
أحدب متزايد Cikakken Wata Tasowa Rana 12 / 29.5
Haske 92%
Cikakken Wata a cikin kwana 3
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad