Ruku'u 405 daga Surah Ghafir ne (ayoyi 10 zuwa 20). Yana ɗauke da ayoyi 11 kuma yana cikin Juz 24.
An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34
Karanta duka cikakken : Kara Ruku'u 405 na Alkur'ani →
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ يُنَادَوْنَ لَمَقْتُ ٱللَّهِ أَكْبَرُ مِن مَّقْتِكُمْ أَنفُسَكُمْ إِذْ تُدْعَوْنَ إِلَى ٱلْإِيمَـٰنِ فَتَكْفُرُونَ ﴿١٠﴾
Lalle waɗanda suka kãfirta, anã kiran su, "Haƙĩƙa, ƙin Allah (a gare ku) shĩ ne mafi girma daga ƙinku ga kanku a lõkacin da ake kiran ku zuwa ga ĩmãni, sai kunã ta kãfircẽwa."
قَالُوا۟ رَبَّنَآ أَمَتَّنَا ٱثْنَتَيْنِ وَأَحْيَيْتَنَا ٱثْنَتَيْنِ فَٱعْتَرَفْنَا بِذُنُوبِنَا فَهَلْ إِلَىٰ خُرُوجٍۢ مِّن سَبِيلٍۢ ﴿١١﴾
Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Kã matar da mu sau biyu, kuma Kã rãyar da mu sau biyu, sabõda haka mun yarda da laifuffukan mu. To, shin, akwai wata hanya zuwa ga fita?"
ذَٰلِكُم بِأَنَّهُۥٓ إِذَا دُعِىَ ٱللَّهُ وَحْدَهُۥ كَفَرْتُمْ ۖ وَإِن يُشْرَكْ بِهِۦ تُؤْمِنُوا۟ ۚ فَٱلْحُكْمُ لِلَّهِ ٱلْعَلِىِّ ٱلْكَبِيرِ ﴿١٢﴾
Wancan sababinsa, lalle (shi ne) idan an kirãyi Allah Shi kaɗai, sai ku kãfirta, kuma idan aka yi shirki game da Shi, sai ku yi ĩmãni. To, hukuncin fa, na Allah Maɗaukaki, Mai girma ne.
هُوَ ٱلَّذِى يُرِيكُمْ ءَايَـٰتِهِۦ وَيُنَزِّلُ لَكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ رِزْقًۭا ۚ وَمَا يَتَذَكَّرُ إِلَّا مَن يُنِيبُ ﴿١٣﴾
Shĩ ne Wanda ke nũna muku ãyõyinSa, kuma Ya saukar da arziki daga sama sabõda ku, kuma bãbu mai yin tunãni fãce mai mayar da al'amari ga Allah.
فَٱدْعُوا۟ ٱللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ ٱلْكَـٰفِرُونَ ﴿١٤﴾
Sabõda haka ku kirãyi Allah, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi, kuma kõ dã kãfirai sun ƙi.
رَفِيعُ ٱلدَّرَجَـٰتِ ذُو ٱلْعَرْشِ يُلْقِى ٱلرُّوحَ مِنْ أَمْرِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦ لِيُنذِرَ يَوْمَ ٱلتَّلَاقِ ﴿١٥﴾
Mai ɗaukaka darajõji (dõmin mũminai), Mai Al'arshi, Yanã jẽfa rũhi daga al'amarinSa a kan wanda Ya so daga bãyinSa, dõmin ya yi gargaɗi kan rãnar gamuwa.
يَوْمَ هُم بَـٰرِزُونَ ۖ لَا يَخْفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِنْهُمْ شَىْءٌۭ ۚ لِّمَنِ ٱلْمُلْكُ ٱلْيَوْمَ ۖ لِلَّهِ ٱلْوَٰحِدِ ٱلْقَهَّارِ ﴿١٦﴾
Rãnar da suke bayyanannu, bãbu wani abu daga gare su wanda yake iya bõyuwa ga Allah. "Mulki ga wa ya ke a yau?" Yana ga Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa.
ٱلْيَوْمَ تُجْزَىٰ كُلُّ نَفْسٍۭ بِمَا كَسَبَتْ ۚ لَا ظُلْمَ ٱلْيَوْمَ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلْحِسَابِ ﴿١٧﴾
Yau anã sãka wa kõwane rai a game da abin da ya aikata, bãbu zãlunci a yau. Lalle Allah Mai gaggawar hisãbi ne.
وَأَنذِرْهُمْ يَوْمَ ٱلْـَٔازِفَةِ إِذِ ٱلْقُلُوبُ لَدَى ٱلْحَنَاجِرِ كَـٰظِمِينَ ۚ مَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنْ حَمِيمٍۢ وَلَا شَفِيعٍۢ يُطَاعُ ﴿١٨﴾
Kuma ka yi musu gargaɗi kan rãnar (Sã'a) makusanciya, a lõkacin da zukãta suke mãsu cika da bakin ciki, ga maƙõsansu. Bãbu wani masõyi ga azzãlumai, kuma bãbu wani mai cẽto da zã a yi wa dã'a (ga cẽtonsu).
يَعْلَمُ خَآئِنَةَ ٱلْأَعْيُنِ وَمَا تُخْفِى ٱلصُّدُورُ ﴿١٩﴾
(Allah) Ya san yaudarar idãnu da abin da ƙirãza ke ɓõyẽwa.
وَٱللَّهُ يَقْضِى بِٱلْحَقِّ ۖ وَٱلَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَقْضُونَ بِشَىْءٍ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْبَصِيرُ ﴿٢٠﴾
Kuma Allah Shĩ ke yin hukunci da gaskiya, waɗannan da kuke kira, waninSa, bã su yin hukunci da kõme. Lalle Allah, Shĩ ne Mai ji, Mai gani.