Kara Ruku'u 425 na Alkur'ani

Ruku'u 425 daga Surah Az-Zukhruf ne (ayoyi 16 zuwa 25). Yana ɗauke da ayoyi 10 kuma yana cikin Juz 25.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Ruku 425 a cikin Alkur'ani

10
ayoyi
1
Surah
25
Juz
v.16 – v.25
Ayoyi

Surori a cikin Ruku 425

الزخرف · Juz 25
Kewaya
Alamomi
Sauti
Hadda
Nuni
Shafi 490
◄ Ruku'u 425 ►
سورة الزخرف
Juz 25 30.9% (76/246)
Hizb 49 90.5% (76/84)

أَمِ ٱتَّخَذَ مِمَّا يَخْلُقُ بَنَاتٍۢ وَأَصْفَىٰكُم بِٱلْبَنِينَ ﴿16﴾

Kõ zã Ya ɗauki 'ya'ya mãtã daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zãɓe ku da ɗiya maza?

وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِمَا ضَرَبَ لِلرَّحْمَـٰنِ مَثَلًۭا ظَلَّ وَجْهُهُۥ مُسْوَدًّۭا وَهُوَ كَظِيمٌ ﴿17﴾

Alhãli kuwa idan an bãyar da bushãra ga ɗayansu da abin da ya buga misãli da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tanã wadda aka baƙanta launinta, kuma yanã cike da baƙin ciki.

أَوَمَن يُنَشَّؤُا۟ فِى ٱلْحِلْيَةِ وَهُوَ فِى ٱلْخِصَامِ غَيْرُ مُبِينٍۢ ﴿18﴾

Ashe, kuma (Allah zai zãɓi) wanda ake rẽno a cikin ƙawa alhãli kuwa gã shi a husũma bã mai iya bayyanawar magana ba?

وَجَعَلُوا۟ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةَ ٱلَّذِينَ هُمْ عِبَـٰدُ ٱلرَّحْمَـٰنِ إِنَـٰثًا ۚ أَشَهِدُوا۟ خَلْقَهُمْ ۚ سَتُكْتَبُ شَهَـٰدَتُهُمْ وَيُسْـَٔلُونَ ﴿19﴾

Kuma suka mayar da malã'iku ('yã'ya) mãtã, alhãli kuwa sũ, waɗanda suke bãyin (Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? zã a rubũta shaidarsu kuma a tambaye su.

وَقَالُوا۟ لَوْ شَآءَ ٱلرَّحْمَـٰنُ مَا عَبَدْنَـٰهُم ۗ مَّا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِنْ هُمْ إِلَّا يَخْرُصُونَ ﴿20﴾

Kuma suka ce: "Dã Mai rahama ya so, dã ba mu bauta musu ba." Bã su da wani ilmi game da wancan! Bãbu abin da suke yi fãce yanki-faɗi.

أَمْ ءَاتَيْنَـٰهُمْ كِتَـٰبًۭا مِّن قَبْلِهِۦ فَهُم بِهِۦ مُسْتَمْسِكُونَ ﴿21﴾

Kõ Mun bã su wani littãfi ne a gabãninsa (Alƙur'ãni) sabõda haka da shĩ suke riƙe?

بَلْ قَالُوٓا۟ إِنَّا وَجَدْنَآ ءَابَآءَنَا عَلَىٰٓ أُمَّةٍۢ وَإِنَّا عَلَىٰٓ ءَاثَـٰرِهِم مُّهْتَدُونَ ﴿22﴾

Ã'a, sun ce dai, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini (na al'ãda) kuma lalle mũ, a kan gurãbunsu muke mãsu nẽman shiryuwa."

وَكَذَٰلِكَ مَآ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ فِى قَرْيَةٍۢ مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتْرَفُوهَآ إِنَّا وَجَدْنَآ ءَابَآءَنَا عَلَىٰٓ أُمَّةٍۢ وَإِنَّا عَلَىٰٓ ءَاثَـٰرِهِم مُّقْتَدُونَ ﴿23﴾

Kuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabãninka, a cikin wata alƙarya, fãce mani'imtanta sun ce, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mũ, mãsu kõyi nea kan gurãbunsu."

۞ قَـٰلَ أَوَلَوْ جِئْتُكُم بِأَهْدَىٰ مِمَّا وَجَدتُّمْ عَلَيْهِ ءَابَآءَكُمْ ۖ قَالُوٓا۟ إِنَّا بِمَآ أُرْسِلْتُم بِهِۦ كَـٰفِرُونَ ﴿24﴾

(Sai mai gargaɗin) ya ce: "Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sãmi ubanninku a kansa ba?" Suka ce, "Lalle mũ dai mãsu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi."

فَٱنتَقَمْنَا مِنْهُمْ ۖ فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلْمُكَذِّبِينَ ﴿25﴾

Sabõda haka Muka yi musu azãbar rãmuwa. To, ka dũbi yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa take.

بسم الله الرحمن الرحيم Asa 27 Rabi' al-Thani
السبت 27 ربيع الآخر
هلال متناقص Gajimaren Raguwa Rana 28.8 / 29.5
Haske 1%
Wata Sabo a cikin kwana 1
سبحان الله وبحمده Tsarkin Allah da godiyarSa

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah