Kara Ruku'u 444 na Alkur'ani

Ruku'u 444 daga Surah Muhammad ne (ayoyi 20 zuwa 28). Yana ɗauke da ayoyi 9 kuma yana cikin Juz 26.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Ruku 444 a cikin Alkur'ani

9
ayoyi
1
Surah
26
Juz
v.20 – v.28
Ayoyi

Surori a cikin Ruku 444

محمد · Juz 26
Kewaya
Alamomi
Sauti
Hadda
Nuni
Shafi 509
◄ Ruku'u 444 ►
سورة محمد
Juz 26 27.7% (54/195)
Hizb 51 60.0% (54/90)

وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَوْلَا نُزِّلَتْ سُورَةٌۭ ۖ فَإِذَآ أُنزِلَتْ سُورَةٌۭ مُّحْكَمَةٌۭ وَذُكِرَ فِيهَا ٱلْقِتَالُ ۙ رَأَيْتَ ٱلَّذِينَ فِى قُلُوبِهِم مَّرَضٌۭ يَنظُرُونَ إِلَيْكَ نَظَرَ ٱلْمَغْشِىِّ عَلَيْهِ مِنَ ٱلْمَوْتِ ۖ فَأَوْلَىٰ لَهُمْ ﴿20﴾

Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cẽwa: "Don mẽne ne ba a saukar da wata sũra ba? "To idan aka saukar da wata sũra, bayyananna, kuma aka ambaci yãƙi a cikinta, zã ka ga waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukatansu sunã kallo zuwa gare ka, irin kallon wanda aka rufe da mãgãgi sabõda mutuwa. To, abin da yake mafĩfĩci a gare su:

طَاعَةٌۭ وَقَوْلٌۭ مَّعْرُوفٌۭ ۚ فَإِذَا عَزَمَ ٱلْأَمْرُ فَلَوْ صَدَقُوا۟ ٱللَّهَ لَكَانَ خَيْرًۭا لَّهُمْ ﴿21﴾

Yin ɗã'a da magana mai kyau. Sa'an nan idan al'marin ya ƙullu, to, dã sun yi wa Allah gaskiya, lalle dã ya kasance mafifi ci a gare su.

فَهَلْ عَسَيْتُمْ إِن تَوَلَّيْتُمْ أَن تُفْسِدُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ وَتُقَطِّعُوٓا۟ أَرْحَامَكُمْ ﴿22﴾

To, shin, kunã fãtan idan kun jũya (daga umurnin) zã ku yi ɓarna a cikin ƙasã, kuma ku yan yanke zumuntarku?

أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَعَنَهُمُ ٱللَّهُ فَأَصَمَّهُمْ وَأَعْمَىٰٓ أَبْصَـٰرَهُمْ ﴿23﴾

Waɗannan sũ ne waɗanda Allah Ya la'anẽ su, sa'an nan Ya kurumtar da su, kuma Ya makantar da ganinsu.

أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ ٱلْقُرْءَانَ أَمْ عَلَىٰ قُلُوبٍ أَقْفَالُهَآ ﴿24﴾

Shin to, bã zã su, kula da Alƙur'ãni ba, kõ kuwa a bin zukã tansu akwai makullansu?

إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱرْتَدُّوا۟ عَلَىٰٓ أَدْبَـٰرِهِم مِّنۢ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ ٱلْهُدَى ۙ ٱلشَّيْطَـٰنُ سَوَّلَ لَهُمْ وَأَمْلَىٰ لَهُمْ ﴿25﴾

lalle ne, waɗanda suka kõma bãya a kan dugãdugansu a bãyan shiryuwa tã bayyana a gare su, Shaiɗan ne ya ƙawãta musu (haka), kuma ya yi musu shibta.

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوا۟ لِلَّذِينَ كَرِهُوا۟ مَا نَزَّلَ ٱللَّهُ سَنُطِيعُكُمْ فِى بَعْضِ ٱلْأَمْرِ ۖ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ إِسْرَارَهُمْ ﴿26﴾

Wancan, dõmin lalle sũ sun ce wa waɗanda suka ƙi abin da Allah Ya saukar: "Za mu yi muku ɗã'ã ga sãshen al'amarin," alhãli kuwa Allah Yanã sane da gãnawarsu ta asĩri.

فَكَيْفَ إِذَا تَوَفَّتْهُمُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ يَضْرِبُونَ وُجُوهَهُمْ وَأَدْبَـٰرَهُمْ ﴿27﴾

To, yãya hãlinsu yake a lõkacin da malã'iku ke karɓar rãyukansu, sunã dũkan fuskõkinsu da ɗuwaiwansu?

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ ٱتَّبَعُوا۟ مَآ أَسْخَطَ ٱللَّهَ وَكَرِهُوا۟ رِضْوَٰنَهُۥ فَأَحْبَطَ أَعْمَـٰلَهُمْ ﴿28﴾

Wannan, dõmin lalle sũ sun bi abin da ya, fusãtar da Allah kuma sun ƙi yardarSa, sabõda haka Ya ɓãta ayyukansu.

بسم الله الرحمن الرحيم Alh 25 Rabi' al-Thani
الخميس 25 ربيع الآخر
هلال متناقص Gajimaren Raguwa Rana 26.9 / 29.5
Haske 8%
Wata Sabo a cikin kwana 3
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah