Ruku'u 462 daga Surah An-Najm ne (ayoyi 33 zuwa 62). Yana ɗauke da ayoyi 30 kuma yana cikin Juz 27.
An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34
Karanta duka cikakken : Kara Ruku'u 462 na Alkur'ani →
أَفَرَءَيْتَ ٱلَّذِى تَوَلَّىٰ ﴿٣٣﴾
Shin, ka ga wannan da ya jũya baya?
وَأَعْطَىٰ قَلِيلًۭا وَأَكْدَىٰٓ ﴿٣٤﴾
Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa?
أَعِندَهُۥ عِلْمُ ٱلْغَيْبِ فَهُوَ يَرَىٰٓ ﴿٣٥﴾
Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin?
أَمْ لَمْ يُنَبَّأْ بِمَا فِى صُحُفِ مُوسَىٰ ﴿٣٦﴾
Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã?
وَإِبْرَٰهِيمَ ٱلَّذِى وَفَّىٰٓ ﴿٣٧﴾
Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari?
أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٌۭ وِزْرَ أُخْرَىٰ ﴿٣٨﴾
Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani.
وَأَن لَّيْسَ لِلْإِنسَـٰنِ إِلَّا مَا سَعَىٰ ﴿٣٩﴾
Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata.
وَأَنَّ سَعْيَهُۥ سَوْفَ يُرَىٰ ﴿٤٠﴾
Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi.
ثُمَّ يُجْزَىٰهُ ٱلْجَزَآءَ ٱلْأَوْفَىٰ ﴿٤١﴾
Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?
وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلْمُنتَهَىٰ ﴿٤٢﴾
Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take?
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَضْحَكَ وَأَبْكَىٰ ﴿٤٣﴾
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَمَاتَ وَأَحْيَا ﴿٤٤﴾
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar.
وَأَنَّهُۥ خَلَقَ ٱلزَّوْجَيْنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰ ﴿٤٥﴾
Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.
مِن نُّطْفَةٍ إِذَا تُمْنَىٰ ﴿٤٦﴾
Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.
وَأَنَّ عَلَيْهِ ٱلنَّشْأَةَ ٱلْأُخْرَىٰ ﴿٤٧﴾
Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَغْنَىٰ وَأَقْنَىٰ ﴿٤٨﴾
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.
وَأَنَّهُۥ هُوَ رَبُّ ٱلشِّعْرَىٰ ﴿٤٩﴾
Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira.
وَأَنَّهُۥٓ أَهْلَكَ عَادًا ٱلْأُولَىٰ ﴿٥٠﴾
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.
وَثَمُودَا۟ فَمَآ أَبْقَىٰ ﴿٥١﴾
Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.
وَقَوْمَ نُوحٍۢ مِّن قَبْلُ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ هُمْ أَظْلَمَ وَأَطْغَىٰ ﴿٥٢﴾
Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.
وَٱلْمُؤْتَفِكَةَ أَهْوَىٰ ﴿٥٣﴾
Da waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kãyar da su.
فَغَشَّىٰهَا مَا غَشَّىٰ ﴿٥٤﴾
Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.
فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ ﴿٥٥﴾
To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake yin shakka?
هَـٰذَا نَذِيرٌۭ مِّنَ ٱلنُّذُرِ ٱلْأُولَىٰٓ ﴿٥٦﴾
wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.
أَزِفَتِ ٱلْـَٔازِفَةُ ﴿٥٧﴾
Makusanciya fa, tã yi kusa.
لَيْسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ كَاشِفَةٌ ﴿٥٨﴾
Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.
أَفَمِنْ هَـٰذَا ٱلْحَدِيثِ تَعْجَبُونَ ﴿٥٩﴾
Shin, kuma daga wannan lãbãri kuke mãmãki?
وَتَضْحَكُونَ وَلَا تَبْكُونَ ﴿٦٠﴾
Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?
وَأَنتُمْ سَـٰمِدُونَ ﴿٦١﴾
Alhãli kunã mãsu wãsã?
فَٱسْجُدُوا۟ لِلَّهِ وَٱعْبُدُوا۟ ۩ ﴿٦٢﴾
To, ku yi tawãli'u ga Allah, kuma ku bauta (masa).