Kara Shafi 305 na Alkur'ani

Shafi 305 na Mushaf yana ɗauke da ayoyi 11. Yana cikin Juz 16, Hizb 31.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Shafi 305 a cikin Alkur'ani

11
ayoyi
16
Juz
31
Hizb
1
Surah

Surori a cikin Shafi 305

مريم · Juz 16
Juz 16
Shafi 305
سورة مريم
Juz 16 13.4% (36/269)
Hizb 31 26.9% (36/134)

كٓهيعٓصٓ ﴿١﴾

K̃.H. Y.I. Ṣ̃.

ذِكْرُ رَحْمَتِ رَبِّكَ عَبْدَهُۥ زَكَرِيَّآ ﴿٢﴾

Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya.

إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُۥ نِدَآءً خَفِيًّۭا ﴿٣﴾

A lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, kira ɓõyayye.

قَالَ رَبِّ إِنِّى وَهَنَ ٱلْعَظْمُ مِنِّى وَٱشْتَعَلَ ٱلرَّأْسُ شَيْبًۭا وَلَمْ أَكُنۢ بِدُعَآئِكَ رَبِّ شَقِيًّۭا ﴿٤﴾

Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji!"

وَإِنِّى خِفْتُ ٱلْمَوَٰلِىَ مِن وَرَآءِى وَكَانَتِ ٱمْرَأَتِى عَاقِرًۭا فَهَبْ لِى مِن لَّدُنكَ وَلِيًّۭا ﴿٥﴾

"Kuma lalle nĩ, na ji tsõron dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa."

يَرِثُنِى وَيَرِثُ مِنْ ءَالِ يَعْقُوبَ ۖ وَٱجْعَلْهُ رَبِّ رَضِيًّۭا ﴿٦﴾

"Ya gãjẽ ni, kuma ya yi gãdo daga gidan Yãƙũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yã Ubangiji!"

يَـٰزَكَرِيَّآ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَـٰمٍ ٱسْمُهُۥ يَحْيَىٰ لَمْ نَجْعَل لَّهُۥ مِن قَبْلُ سَمِيًّۭا ﴿٧﴾

(Allah Ya karɓa) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni."

قَالَ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِى غُلَـٰمٌۭ وَكَانَتِ ٱمْرَأَتِى عَاقِرًۭا وَقَدْ بَلَغْتُ مِنَ ٱلْكِبَرِ عِتِيًّۭا ﴿٨﴾

Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuƙa ta tsũfa?"

قَالَ كَذَٰلِكَ قَالَ رَبُّكَ هُوَ عَلَىَّ هَيِّنٌۭ وَقَدْ خَلَقْتُكَ مِن قَبْلُ وَلَمْ تَكُ شَيْـًۭٔا ﴿٩﴾

Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba."

قَالَ رَبِّ ٱجْعَل لِّىٓ ءَايَةًۭ ۚ قَالَ ءَايَتُكَ أَلَّا تُكَلِّمَ ٱلنَّاسَ ثَلَـٰثَ لَيَالٍۢ سَوِيًّۭا ﴿١٠﴾

Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai."

فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوْمِهِۦ مِنَ ٱلْمِحْرَابِ فَأَوْحَىٰٓ إِلَيْهِمْ أَن سَبِّحُوا۟ بُكْرَةًۭ وَعَشِيًّۭا ﴿١١﴾

Sai ya fita a kan mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma."

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 20 Safar
الأربعاء 20 صفر
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 21.9 / 29.5
Haske 53%
Wata Sabo a cikin kwana 8
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah