Kara Shafi 502 na Alkur'ani

Shafi 502 na Mushaf yana ɗauke da ayoyi 10. Yana cikin Juz 25, Hizb 50.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Shafi 502 a cikin Alkur'ani

10
ayoyi
25
Juz
50
Hizb
2
Surah
الجاثية · Juz 25
Juz 25
Shafi 502
سورة الجاثية
Juz 25 98.0% (241/246)
Hizb 50 96.9% (157/162)

وَبَدَا لَهُمْ سَيِّـَٔاتُ مَا عَمِلُوا۟ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ ﴿٣٣﴾

Kuma mũnanan abin da suka aikata ya bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu.

وَقِيلَ ٱلْيَوْمَ نَنسَىٰكُمْ كَمَا نَسِيتُمْ لِقَآءَ يَوْمِكُمْ هَـٰذَا وَمَأْوَىٰكُمُ ٱلنَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّـٰصِرِينَ ﴿٣٤﴾

Kuma aka ce: "A yau zã Mu manta da ku, kamar yadda kuka manta da gamuwa da yininku wannan. Kuma mãkõmarku wutã ce, Kuma bã ku da waɗansu mãsu taimako.

ذَٰلِكُم بِأَنَّكُمُ ٱتَّخَذْتُمْ ءَايَـٰتِ ٱللَّهِ هُزُوًۭا وَغَرَّتْكُمُ ٱلْحَيَوٰةُ ٱلدُّنْيَا ۚ فَٱلْيَوْمَ لَا يُخْرَجُونَ مِنْهَا وَلَا هُمْ يُسْتَعْتَبُونَ ﴿٣٥﴾

"Wancan dõmin lalle kũ, kun riƙi ãyõyin Allah da izgili, Kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe ku. To, a yau bã zã su fita daga gare ta ba, Kuma bã zã su zama waɗanda ake nẽman yardarsu ba."

فَلِلَّهِ ٱلْحَمْدُ رَبِّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَرَبِّ ٱلْأَرْضِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ ﴿٣٦﴾

Sabõda haka, gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin sammai, kuma Ubangijin ƙasã, Ubangijin halittu.

وَلَهُ ٱلْكِبْرِيَآءُ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۖ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ ﴿٣٧﴾

Kuma gare Shi girma yake, a cikin sammai da ƙasã, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Hikima.

حمٓ ﴿١﴾

Ḥ. M̃.

تَنزِيلُ ٱلْكِتَـٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلْعَزِيزِ ٱلْحَكِيمِ ﴿٢﴾

Saukar da littafi daga Allah, Mabuwãyi, Mai hikima yake.

مَا خَلَقْنَا ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَآ إِلَّا بِٱلْحَقِّ وَأَجَلٍۢ مُّسَمًّۭى ۚ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ عَمَّآ أُنذِرُوا۟ مُعْرِضُونَ ﴿٣﴾

Ba Mu halitta sammai da ƙasa ba, da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da wani ajali ambatacce, kuma waɗanda suka kãfirta, mãsu bijirẽwa ne daga abin da aka yi musu gargaɗi (da shi).

قُلْ أَرَءَيْتُم مَّا تَدْعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَرُونِى مَاذَا خَلَقُوا۟ مِنَ ٱلْأَرْضِ أَمْ لَهُمْ شِرْكٌۭ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ ۖ ٱئْتُونِى بِكِتَـٰبٍۢ مِّن قَبْلِ هَـٰذَآ أَوْ أَثَـٰرَةٍۢ مِّنْ عِلْمٍ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ ﴿٤﴾

Ka ce: "Shin, kun gani, abin da kuke kira, wanda yake baicin Allah? Ku nũna mini, menene suka halitta daga ƙasa? Kõ kuwa sunã da tãrayya a cikin sammai? Ku zo mini da wani littãfi na gabãnin wannan (Alƙur'ãni) kõ wata alãma daga wani ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya."

وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّن يَدْعُوا۟ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَن لَّا يَسْتَجِيبُ لَهُۥٓ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ وَهُمْ عَن دُعَآئِهِمْ غَـٰفِلُونَ ﴿٥﴾

Kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ke kiran wanin Allah wanda da bã zai karɓa masa ba, bar Rãnar Kyama, alhãli sũ (waɗanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiransu?

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 20 Safar
الأربعاء 20 صفر
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 21.9 / 29.5
Haske 52%
Wata Sabo a cikin kwana 8
سبحان الله Subhanallah - Tsarkin Allah