Kara Ruku'u 430 na Alkur'ani

Ruku'u 430 daga Surah Az-Zukhruf ne (ayoyi 68 zuwa 89). Yana ɗauke da ayoyi 22 kuma yana cikin Juz 25.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Ruku 430 a cikin Alkur'ani

22
ayoyi
1
Surah
25
Juz
v.68 – v.89
Ayoyi

Surori a cikin Ruku 430

الزخرف · Juz 25
Kewaya
Alamomi
Sauti
Hadda
Nuni
Shafi 494
◄ Ruku'u 430 ►
سورة الزخرف
Juz 25 52.0% (128/246)
Hizb 50 27.2% (44/162)

يَـٰعِبَادِ لَا خَوْفٌ عَلَيْكُمُ ٱلْيَوْمَ وَلَآ أَنتُمْ تَحْزَنُونَ ﴿68﴾

Ya bãyĩNa! Bãbu tsõro a kanku a yau, kuma bã zã ku yi baƙin ciki ba.

ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا وَكَانُوا۟ مُسْلِمِينَ ﴿69﴾

Waɗanda suka yi ĩmãni da ãyõyinMu, kuma suka kasance mãsu sallamawar al'amari (ga Allah).

ٱدْخُلُوا۟ ٱلْجَنَّةَ أَنتُمْ وَأَزْوَٰجُكُمْ تُحْبَرُونَ ﴿70﴾

Ku shiga Aljanna, kũ da mãtan aurenku, anã girmama ku.

يُطَافُ عَلَيْهِم بِصِحَافٍۢ مِّن ذَهَبٍۢ وَأَكْوَابٍۢ ۖ وَفِيهَا مَا تَشْتَهِيهِ ٱلْأَنفُسُ وَتَلَذُّ ٱلْأَعْيُنُ ۖ وَأَنتُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ ﴿71﴾

Anã kẽwayãwa a kansu da akussa na zĩnãriya da kõfuna, alhãli kuwa a cikinsu akwai abin da rãyuka ke marmari kuma idãnu su ji dãɗi, kuma kũ, a cikinta (Aljannar), madawwama ne.

وَتِلْكَ ٱلْجَنَّةُ ٱلَّتِىٓ أُورِثْتُمُوهَا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ ﴿72﴾

Kuma waccan ita ce Aljannar, wannan da aka gãdar da ku ita sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa.

لَكُمْ فِيهَا فَـٰكِهَةٌۭ كَثِيرَةٌۭ مِّنْهَا تَأْكُلُونَ ﴿73﴾

Kunã sãmu, a cikinta, 'yã'yan itãcen marmari mãsu yawa, daga cikinsu kuke ci.

إِنَّ ٱلْمُجْرِمِينَ فِى عَذَابِ جَهَنَّمَ خَـٰلِدُونَ ﴿74﴾

Lalle mãsu laifi madawwama ne a cikin azãbar Jahannama.

لَا يُفَتَّرُ عَنْهُمْ وَهُمْ فِيهِ مُبْلِسُونَ ﴿75﴾

Bã a sauƙaƙar da ita (azãbar) daga gare su, alhãli kuwa sũ, a cikinta, mãsu kãsa magana ne.

وَمَا ظَلَمْنَـٰهُمْ وَلَـٰكِن كَانُوا۟ هُمُ ٱلظَّـٰلِمِينَ ﴿76﴾

Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sũ ne suka kasance azzãlumai.

وَنَادَوْا۟ يَـٰمَـٰلِكُ لِيَقْضِ عَلَيْنَا رَبُّكَ ۖ قَالَ إِنَّكُم مَّـٰكِثُونَ ﴿77﴾

Kuma suka yi kira, "Ya Mãliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana " (Mãliku) ya ce: "Lalle kũ mazauna ne."

لَقَدْ جِئْنَـٰكُم بِٱلْحَقِّ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَكُمْ لِلْحَقِّ كَـٰرِهُونَ ﴿78﴾

Lalle ne, haƙĩƙa, Mun jẽ muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku mãsu ƙi ga gaskiyar ne.

أَمْ أَبْرَمُوٓا۟ أَمْرًۭا فَإِنَّا مُبْرِمُونَ ﴿79﴾

Kõ kuma sun tukka wani al'amari ne? To, lalle Mũ, Mãsu tukkãwa ne.

أَمْ يَحْسَبُونَ أَنَّا لَا نَسْمَعُ سِرَّهُمْ وَنَجْوَىٰهُم ۚ بَلَىٰ وَرُسُلُنَا لَدَيْهِمْ يَكْتُبُونَ ﴿80﴾

Ko sunã zaton lalle Mũ, bã Mu jin asĩrinsu da gãnãwarsu? Na'am! Kuma manzannin Mu na tãre da su sunã rubũtãwa.

قُلْ إِن كَانَ لِلرَّحْمَـٰنِ وَلَدٌۭ فَأَنَا۠ أَوَّلُ ٱلْعَـٰبِدِينَ ﴿81﴾

Ka ce: "Idan har akwai ɗã ga Mai rahama, to, nĩ ne farkon mãsu bauta (wa ɗan)."

سُبْحَـٰنَ رَبِّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ رَبِّ ٱلْعَرْشِ عَمَّا يَصِفُونَ ﴿82﴾

Tsarkin Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al'arshi, ya tabbata daga abin da suke sifantãwa.

فَذَرْهُمْ يَخُوضُوا۟ وَيَلْعَبُوا۟ حَتَّىٰ يُلَـٰقُوا۟ يَوْمَهُمُ ٱلَّذِى يُوعَدُونَ ﴿83﴾

Sabõda haka, ka ƙyãlẽ su, su kũtsa kuma su yi wãsã har su haɗu da yininsu, wanda ake yi musu wa'adi da shi.

وَهُوَ ٱلَّذِى فِى ٱلسَّمَآءِ إِلَـٰهٌۭ وَفِى ٱلْأَرْضِ إِلَـٰهٌۭ ۚ وَهُوَ ٱلْحَكِيمُ ٱلْعَلِيمُ ﴿84﴾

Kuma Shĩ ne wanda ke abin bautãwa a sama kuma abin bautãwa a ƙasa, kuma, Shĩ ne Mai hikima, Masani.

وَتَبَارَكَ ٱلَّذِى لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَعِندَهُۥ عِلْمُ ٱلسَّاعَةِ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ ﴿85﴾

Kuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasã abin da ke a tsakãninsu tã bayyana, kuma a wurinSa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.

وَلَا يَمْلِكُ ٱلَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِهِ ٱلشَّفَـٰعَةَ إِلَّا مَن شَهِدَ بِٱلْحَقِّ وَهُمْ يَعْلَمُونَ ﴿86﴾

Kuma waɗanda suke kira baicinSa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane (da haka).

وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَهُمْ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُ ۖ فَأَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ ﴿87﴾

Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su?

وَقِيلِهِۦ يَـٰرَبِّ إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ قَوْمٌۭ لَّا يُؤْمِنُونَ ﴿88﴾

Kuma da (ilmin) maganarSa (Annabi) "Ya Ubangijĩna! Lalle waɗannan mutãne ne waɗanda bã zã su yi ĩmãni ba."

فَٱصْفَحْ عَنْهُمْ وَقُلْ سَلَـٰمٌۭ ۚ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ ﴿89﴾

To, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, "salãmã." Sa'an nan kuma zã su sani.

بسم الله الرحمن الرحيم Jum 26 Rabi' al-Thani
الجمعة 26 ربيع الآخر
هلال متناقص Gajimaren Raguwa Rana 27.9 / 29.5
Haske 3%
Wata Sabo a cikin kwana 2
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah