Kara Ruku'u 513 na Alkur'ani

Ruku'u 513 daga Surah Al-Qiyama ne (ayoyi 31 zuwa 40). Yana ɗauke da ayoyi 10 kuma yana cikin Juz 29.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Ruku 513 a cikin Alkur'ani

10
ayoyi
1
Surah
29
Juz
v.31 – v.40
Ayoyi

Surori a cikin Ruku 513

القيامة · Juz 29
Kewaya
Alamomi
Sauti
Hadda
Nuni
Shafi 578
◄ Ruku'u 513 ►
سورة القيامة
Juz 29 78.9% (340/431)
Hizb 58 59.6% (134/225)

فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ ﴿31﴾

To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!

وَلَـٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ ﴿32﴾

Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!

ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰٓ أَهْلِهِۦ يَتَمَطَّىٰٓ ﴿33﴾

Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.

أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ ﴿34﴾

Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.

ثُمَّ أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰٓ ﴿35﴾

Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.

أَيَحْسَبُ ٱلْإِنسَـٰنُ أَن يُتْرَكَ سُدًى ﴿36﴾

Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?

أَلَمْ يَكُ نُطْفَةًۭ مِّن مَّنِىٍّۢ يُمْنَىٰ ﴿37﴾

Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)

ثُمَّ كَانَ عَلَقَةًۭ فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ ﴿38﴾

Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;

فَجَعَلَ مِنْهُ ٱلزَّوْجَيْنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰٓ ﴿39﴾

Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?

أَلَيْسَ ذَٰلِكَ بِقَـٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحْـِۧىَ ٱلْمَوْتَىٰ ﴿40﴾

Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?

بسم الله الرحمن الرحيم Asa 27 Rabi' al-Thani
السبت 27 ربيع الآخر
هلال متناقص Gajimaren Raguwa Rana 29 / 29.5
Haske 0%
Wata Sabo a cikin kwana 0
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah