Kara Shafi 2 na Alkur'ani

Shafi 2 na Mushaf yana ɗauke da ayoyi 5. Yana cikin Juz 1, Hizb 1.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Shafi 2 a cikin Alkur'ani

5
ayoyi
1
Juz
1
Hizb
1
Surah

Surori a cikin Shafi 2

البقرة · Juz 1
Kewaya
Alamomi
Sauti
Hadda
Nuni
Juz 1
Shafi 2
سورة البقرة
Juz 1 4.7% (7/148)
Hizb 1 8.6% (7/81)

الٓمٓ ﴿1﴾

A. L̃. M̃.

ذَٰلِكَ ٱلْكِتَـٰبُ لَا رَيْبَ ۛ فِيهِ ۛ هُدًۭى لِّلْمُتَّقِينَ ﴿2﴾

Wãncan ne Littãfi, bãbu shakka a cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa.

ٱلَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِٱلْغَيْبِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقْنَـٰهُمْ يُنفِقُونَ ﴿3﴾

Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa.

وَٱلَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيْكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبْلِكَ وَبِٱلْـَٔاخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ ﴿4﴾

Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni.

أُو۟لَـٰٓئِكَ عَلَىٰ هُدًۭى مِّن رَّبِّهِمْ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُفْلِحُونَ ﴿5﴾

Waɗannan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara.

بسم الله الرحمن الرحيم Lah 7 Rabi' al-Thani
الأحد 7 ربيع الآخر
التربيع الأول Kwata na Farko Rana 8.2 / 29.5
Haske 59%
Cikakken Wata a cikin kwana 7
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah