Da a ce ana bawa mutane abu saboda ikirarin cewa nasu ne, da da yawa daga cikin mutane sun…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Da a ce ana bawa mutane abu saboda ikirarin cewa nasu ne, da da yawa daga cikin mutane sun…
Wanda ya ruwaito hadisin: Baihaki da wasu suka ruwaito shi kamar haka, kuma sashensa yana cikin Bukhari da Muslim
Hasan ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Da a ce ana bawa mutane abu saboda ikirarin cewa nasu n…
عَن ابنِ عباسٍ رضي الله عنهما أنَّ رسولَ اللهِ صلي الله عليه وسلم قال: «لَو يُعطَى النّاسُ بدَعواهُم لادَّعَى رِجالٌ أموالَ قَومٍ ودِماءَهُم، لَكِنَّ البَيِّنَةَ على المُدَّعِى، واليَمينَ على مَن أنكَرَ».
Bayanin hadisin: Da a ce ana bawa mutane abu saboda ikirarin cewa nasu n…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa da ace ana bawa mutane saboda kawai mujarradin da'awarsu ba tare da wasu dalilai ba ba kuma tare da wasu alamomi ba to da wasu mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanensu, sai dai gabatar da shaida da dalili ya wajaba akan mai da'awa da abinda yake nema, idan ba shi da shaidu to sai a gabatar da da'awar akan wanda aka kawo karar, idan ya yi inkarinta to ya wajaba ya yi rantsuwa sai ya kubuta.
Koyarwar hadisin: Da a ce ana bawa mutane abu saboda ikirarin cewa nasu n…
- Ibnu Dakikil Id ya ce: Wanann Hadisin asali ne na hukunce-hukunce, kuma mafi girman makoma a lokacin jayayya da husuma.
- Shari'a ta zo dan kare dukiyoyin mutane da jinanensu daga wasa.
- Alkali ba ya hukunci da iliminsa kawai, yana komawa ne zuwa ga shaidu.
- Dukkan wanda ya yi wata da'awa wacce ta wofinta daga hujja to ita abar watsarwa ce, daidai ne ta kasance a cikin hakkoki ne da mu'amaloli ko a cikin mas'alolin imani da sani.
Rukunan :
ALƘALANCI
· ƘARARRAKI DA SHEDU
· FIƘHU DA USULU
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad