Wanda ya yi alwala irin wannan alwalar tawa sannan ya yi sallah raka'a biyu bai zantar da …

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Wanda ya yi alwala irin wannan alwalar tawa sannan ya yi sallah raka'a biyu bai zantar da …

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Wanda ya yi alwala irin wannan alwalar tawa sannan ya y…

عَنْ ‌حُمْرَانَ مَوْلَى عُثْمَانَ بْنِ عَفَّانَ رضي الله عنه: أَنَّهُ رَأَى عُثْمَانَ بْنَ عَفَّانَ دَعَا بِوَضُوءٍ، فَأَفْرَغَ عَلَى يَدَيْهِ مِنْ إِنَائِهِ، فَغَسَلَهُمَا ثَلَاثَ مَرَّاتٍ، ثُمَّ أَدْخَلَ يَمِينَهُ فِي الْوَضُوءِ، ثُمَّ تَمَضْمَضَ وَاسْتَنْشَقَ وَاسْتَنْثَرَ، ثُمَّ غَسَلَ وَجْهَهُ ثَلَاثًا، وَيَدَيْهِ إِلَى الْمِرْفَقَيْنِ ثَلَاثًا، ثُمَّ مَسَحَ بِرَأْسِهِ، ثُمَّ غَسَلَ كُلَّ رِجْلٍ ثَلَاثًا، ثُمَّ قَالَ: رَأَيْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَتَوَضَّأُ نَحْوَ وُضُوئِي هَذَا، وَقَالَ: «مَنْ تَوَضَّأَ نَحْوَ وُضُوئِي هَذَا ثُمَّ صَلَّى رَكْعَتَيْنِ لَا يُحَدِّثُ فِيهِمَا نَفْسَهُ غَفَرَ اللهُ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ».

Bayanin hadisin: Wanda ya yi alwala irin wannan alwalar tawa sannan ya y…

Sayyidina Usman - Allah Ya yarda da shi - ya karantar da siffar alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a aikace; don ya zama mafi fitowa ɓaro-ɓaro, sai ya nemi ruwa a ƙwarya, sai ya zuba a hannayensa sau uku, bayan haka ya shigar da hannunsa na dama a cikin ƙwaryar, sai ya ɗebo ruwa daga cikinta sai ya kurkura shi a bakinsa, sannan ya fitar da shi, sannan ya shaki ruwan da numfashinsa zuwa cikin hancinsa, sannan ya fitar da shi ya face, sannan ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya wanke hannayensa tare da gwiwar hannaye sau uku, sannan ya shuɗar da hannunsa a kan kansa suna masu damshi da ruwa sau ɗaya, sannan ya wanke ƙafafuwansa tare da idon sawu sau uku.

Lokacin da ya gama - Allah Ya yarda da shi - sai ya ba su labarin cewa shi ya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi alwala irin wannan alwalar, kuma [Annabi] - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi musu albishir da cewa wanda ya yi irin wannan alwalar, ya yi sallah raka'a biyu, yana mai khushu'i yana mai halarto da zuciyarsa a gaban Ubangijinsa - mai girma da ɗaukaka - a cikinsu, to, Allah Zai yi masa sakayya a kan wannan alwalar cikakkiya da wannan sallar tsarkakiyya da gafarta abin da ya gabata daga zunubansa.

Koyarwar hadisin: Wanda ya yi alwala irin wannan alwalar tawa sannan ya y…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · TSARKI · FIƘHU DA USULU · ALWALA · SIFFAR ALWALA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله وبحمده Tsarkin Allah da godiyarSa

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah