Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi,…

Bayanin hadisin: Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi,…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana faɗa a cikin Hadisi Ƙudsi:

Dukkan aikin Ɗan Adam ana ninka kyakkyawa da kwatankwacinsa goma zuwa ninki ɗari bakwai, sai azimi; shi nawa ne riya ba ta shiga cikinsa, kuma nine zan yi sakayya da shi, sai in kaɗaita da sanin gwargwadan ladansa da kuma ninka kyawawan (ladansa).

Sannan Ya ce: (Azimi garkuwa ne) kuma kariya ne kuma sitira ne kuma katanga ne mai katangewa daga wuta; domin cewa shi kamewa ne daga sha'awowi da afkawa cikin zunubai, wuta kuma abar kewayewa ce da sha'awowi.

(Idan yinin azimin ɗayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa) da yin jima'i da abubuwan gabatarwarsa, ko mummunan zance kai tsaye.

(Kada ya yi zancen banza) da yin husuma da kuma kururuwa.

(Idan wani ya zage shi ko ya yi faɗa da shi) a cikin Ramadan to ya ce: Lallai ni mai azimi ne; wataƙila ya ƙyale shi, idan ya nace sai dai faɗa to a haƙiƙa to sai ya tunkuɗe shi da mafi sauƙi, sai mafi sauƙi kamar wanda ya shigo maka gida.

Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi rantsuwa da wanda ransa yake a hannunSa cewa canzawar bashin bakin mai azimi saboda azimin ya fi daɗi a wurin Allah ranar alƙiyama daga ƙanshin almiski a wurinku, kuma ya fi yawan lada daga almiski abin so gare shi a ranakun juma'a da kuma majalisan zikiri.

Mai azimi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki da su:

Idan zai yi buɗa baki zai yi farin ciki da gushewar yunwarsa da kuma ƙishirwarsa saboda yadda aka halatta masa buda baki.

Kuma zai yi farin ciki da cikar aziminsa da kuma kammala bautarsa, da kuma sauƙi daga Ubangijinsa, da taimako akan aziminsa na gaba.

(Idan ya gamu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da aziminsa) da sakamakonsa da kuma ladansa.

Koyarwar hadisin: Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi,…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · AZUMI · FIƘHU DA USULU · FALALAR AZUMI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah