Duk wanda ya yi E'itikafi tare da ni to yayi a goman karshe domin nagani a wannan daren sa…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Duk wanda ya yi E'itikafi tare da ni to yayi a goman karshe domin nagani a wannan daren sa…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Duk wanda ya yi E'itikafi tare da ni to yayi a goman ka…

عن أبي سعيد الخُدْري رضي الله عنه : «أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يَعْتَكِفُ في العَشْرِ الأَوْسَطِ من رمضان. فاعتكف عامًا، حتى إذا كانت لَيْلَةَ إِحْدَى وَعِشْرِينَ -وهي اللَّيْلَةُ التي يخرج من صَبِيحَتِهَا من اعتكافه- قال: من اعتكف معي فَلْيَعْتَكِفِ العَشْرَ الأَوَاخِرَ فقد أُرِيتُ هَذِهِ اللَّيْلَةَ ثم أُنْسِيتُهَا، وقد رَأَيْتُنِي أَسْجُدُ فِي مَاءٍ وَطِينٍ من صَبِيحَتِهَا، فَالْتَمِسُوهَا فِي العَشْرِ الأَوَاخِرِ، والتمسوها في كل وِتْرٍ. فَمَطَرَتِ السَّمَاءُ تلك الليلة، وكان المسجد على عَرِيشٍ، فَوَكَفَ المسجد، فَأبْصَرَتْ عَيْنَايَ رسول الله صلى الله عليه وسلم وعلى جَبْهَتِهِ أَثَرُ المَاءِ وَالطِّين من صُبْحِ إحْدَى وَعشْرِيْنَ».

Bayanin hadisin: Duk wanda ya yi E'itikafi tare da ni to yayi a goman ka…

Abu Sa'id Al'khudri yana bada labari cewa Annabi ya kasance yana yin I'itikafin goman tsakiya na Azumi don neman daren lailatul kadari, sai wata shekara yayi -kamar yadda ya saba- har sai da adaren Ashirin da daya, ita ce ranar da yake futowa a safiyarta daga I'itikafinsa, sai ya san cewa lallai daren lailatul kadari tana goman karshe, sai yace da Sahabbansa: Duk wanda yayi I'itikafi tare da ni goman tsakiya, to ya zarce da I'itikafinsa, yayi a goman karshe, kuma ya bada labarin cewa Allah yanuna masa ita a Mafarkinsa sannan ya mantar da shi ita, sai dai ya ce kamar yagani a barcin wasu alamominta a cikin wannan shekarar su ne: Sujadarsa a cikin sallar Asuba akan tabo mai ruwa, to Allah ya gasgata Mafarkin Annabinsa, sai akayi ruwa a daren Ashirin da daya kuma ya kasance Masallacinsa an gina shi ne da yayin danga, kuma kututtudabino shi ne ginshikansa kuma rufinsa na ganyen Dabino ne, to sai Masallacin yayi ta zubar ruwa, sai Annabi yayi Sujada a safiyar Ashirin da daya, a cikin ruwa da tabo, Taisir Allam (349) Tanbih Al'afham (3/472) Ta'asis Al'ahkam 3/292

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · AZUMI · FIƘHU DA USULU · LI'ITIKAFI · GOMAN ƘARSHE TA RAMADAN

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الحمد لله Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah