Lallai Addini mai sauƙi ne, babu wanda zai tsananta cikinsa face sai ya rinjaye shi, sabod…

Musulunci > Ha > Hadith > Daawa zuwa ga allah > Lallai Addini mai sauƙi ne, babu wanda zai tsananta cikinsa face sai ya rinjaye shi, sabod…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Lallai Addini mai sauƙi ne, babu wanda zai tsananta cik…

Bayanin hadisin: Lallai Addini mai sauƙi ne, babu wanda zai tsananta cik…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa Addinin Musulunci an gina shi akan sauƙaƙawa da sauƙi a dukkan sha’aninsa, sauƙi yana ƙarfafa a lokacin samun gajiyawa da buƙata, kuma domin cewa tsanantawa a ayyuka na Addini da barin sauƙi ƙarshensa shi ne gajiyawa da yankewa daga barin aiki gabaɗayansa ko wani daga ciki. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan tsakatsakiya ba tare da zirfafawa ba; kada bawa ya taƙaita a cikin abinda aka umarce shi da shi, kuma kada ya ɗorawa kansa abinda ba zai iya ba, idan ya gajiya daga cikakken aiki to ya yi aiki akan abinda yake kusa da hakan.

Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi bushara da sakamako mai yawa akan dawwamammen aiki koda kadan ne ga wanda ya gajiya daga aiki cikakke; domin kasawa idan bata kasance daga aikinsa ba to bata lazimtar tauye ladansa.

Yayin da cewa duniya a haƙiƙa gidan tafiya ce da tashi zuwa lahira sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi umarni da neman taimako akan dawwama akan ibada ta hanyar yinta a cikin lokuta uku masu sa nishaɗantarwa:

Na farko: Jijjifi: Da tafiya a farkon yini; tsakanin sallar Asuba da hudowar rana.

Na biyu: Yammaci: Da tafiya bayan karkacewar rana.

Na uku: Duhun dare: Da tafiyar dare gabaɗayansa ko sashinsa, domin cewa aikin dare yafi wahala akan aikin rana sai aka yi umarni da sashinsa da faɗinsa: Da wani abu daga duhun dare.

Koyarwar hadisin: Lallai Addini mai sauƙi ne, babu wanda zai tsananta cik…

Rukunan : DA'AWA ZUWA GA ALLAH · FALALAR MUSULUNCI DA KYAWAWAN ABUBUWANSA · DA'AWA DA HISBA

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah