Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Wanda ya sallaci sallar Asuba, to, zai kasance cikin alƙawarin Allah
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن جُندب بن عبد الله القَسْرِِي رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ صَلَّى صَلَاةَ الصُّبْحِ فَهُوَ فِي ذِمَّةِ اللهِ، فَلَا يَطْلُبَنَّكُمُ اللهُ مِنْ ذِمَّتِهِ بِشَيْءٍ، فَإِنَّهُ مَنْ يَطْلُبْهُ مِنْ ذِمَّتِهِ بِشَيْءٍ يُدْرِكْهُ، ثُمَّ يَكُبَّهُ عَلَى وَجْهِهِ فِي نَارِ جَهَنَّمَ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya sallaci Asuba, to, zai kasance cikin kiyayewar Allah da gadinsa da tsarinsa, kuma Zai yi kariya gareshi, kuma zai yi ɗauki gareshi.
Sannan (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gareshi ya yi gargaɗi game da warware wannan alƙawarin da ɓatashi, ko dai da barin sallar Asuba, ko da bijirowa mai sallatarta da ta'addanci a kansa, to, duk wanda ya aikata haka to haƙiƙa ya keta wannan tsarin, kuma ya cancanci narko mai tsanani na cewa Allah Zai nemeshi saboda abin da ya yi sakaci na haƙƙinsa, wanda kuwa Allah Ya nemeshi Zai kamashi, sannan Ya jefashi a wuta ta fuskarsa.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · FALALAR SALLAH