Babu wani mutum musulmi da sallar farilla zata halarto shi, sai ya kyautata alwalarta da k…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Babu wani mutum musulmi da sallar farilla zata halarto shi, sai ya kyautata alwalarta da k…
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Babu wani mutum musulmi da sallar farilla zata halarto…
Bayanin hadisin: Babu wani mutum musulmi da sallar farilla zata halarto…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa babu wani musulmin da lokacin sallar farilla zai shigo masa, sai ya kyautata alwalarta, ya cikata, sannan ya yi khushu'i a sallarsa ta inda zuciyarsa da gabbansa gaba dayansu zasu zama masu fuskantar Allah masu halarto girmansa, kuma ya cika ayyukan sallah kamar ruku'u da sujjada da waninsa, sai ta zama mai kankarewa ce ga abinda ke gabanta na kananan zunubai, muddin dai bai aikata babban laifi daga manyan laifuka ba, wannan falalar mai mikewa ce iya shudewar zamani kuma a kowacce sallah.
Koyarwar hadisin: Babu wani mutum musulmi da sallar farilla zata halarto…
- Sallah mai kankare zunubai ita ce wacce bawa ya kyautata alwalarta, kuma ya yi ta yana mai khushu'i ya nufi yardar Allah - Madaukakin sarki - da ita.
- Falalar dawwama akan ibadu, kuma cewa su sababine na gafarta kananan zunubai.
- Falalar kyautata alwala, da kyautata sallah da khushu'i a cikinta.
- Muhimmancin nisantar manyan zunubai dan gafarta kananan zunubai.
- Manyan zunubai ba'a kankaresu sai da tuba.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· SALLAH
· FIƘHU DA USULU
· FALALAR SALLAH
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله
Subhanallah - Tsarkin Allah