'Lallai waɗannan sallolin biyu sune mafi nauyin salloli akan munafuki, da kun san abinda k…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > 'Lallai waɗannan sallolin biyu sune mafi nauyin salloli akan munafuki, da kun san abinda k…

Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud da Nasa'i haka Ahmad suka ruwaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: 'Lallai waɗannan sallolin biyu sune mafi nauyin salloli…

Bayanin hadisin: 'Lallai waɗannan sallolin biyu sune mafi nauyin salloli…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi sallar Asuba wata rana, sannan ya yi tambaya: Shin wane ya zo wannan sallar da muka yi? Sahabbai suka ce: A'a. Sannan ya ce: Shin wane ya zo ne? ga wani mutumin daban, Suka ce: A'a. (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lallai sallar Asuba da Issha'i sune mafi nauyin salloli akan munafukai; dan rinjayar kasala a cikinsu, da kuma ƙarancin faruwar riya garesu, tunda ba'a ganinsu a cikin duhu.

Da kun san yaku muminai abinda ke cikin sallolin Asuba da Issha'i na lada da sakamako mai ƙaruwa - domin lada yana kan gwargwadan wahala - da kun zo su koda da jan ciki ne da tafiya akan hannaye da gwiwowi.

Kuma masu sahu na farko a kusancinsu da liman kamar sahun mala'iku ne a kusancinsu ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da muminai suna sanin abinda ke cikin falalar sahun farko da sun yi tsere gare shi . Kuma lallai sallar namiji tare da namiji ita ce mafi girman sakamako da tasiri a sallarsa shi kaɗai, kuma sallarsa tare da maza biyu tafi tare da namiji ɗaya, Sallar da masallatan suka yi yawa a cikinta ita ce mafi soyuwa ga Allah kuma ta fi lada.

Koyarwar hadisin: 'Lallai waɗannan sallolin biyu sune mafi nauyin salloli…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · FALALAR SALLAR JAM'I DA HUKUNCE-HUKUNCENTA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الحمد لله Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah