Cewa ita ta zo da wani ɗanta ƙarami bai fara cin abinci ba zuwa ga Manzon Allah - tsira d…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Cewa ita ta zo da wani ɗanta ƙarami bai fara cin abinci ba zuwa ga Manzon Allah - tsira d…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Cewa ita ta zo da wani ɗanta ƙarami bai fara cin abinc…
Bayanin hadisin: Cewa ita ta zo da wani ɗanta ƙarami bai fara cin abinc…
Ummu Kais bintu Mihsan - Allah Ya yarda da shi - ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani ɗanta wanda bai fara cin abinci ba saboda ƙanƙantar shekarunsa, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya zaunar da shi a ƙirjinsa, sai yaron ya yi fitsari akan tufafinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya sa a kawo masa ruwa, sai ya yayyafa ruwan akan tufafinsa bai wanke tufafin ba.
Koyarwar hadisin: Cewa ita ta zo da wani ɗanta ƙarami bai fara cin abinc…
- Kyawawan Ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabata agare shi - mai girma, da kuma tawali'unsa mai yawa.
- An so kyautata kyakkyawar mu'amala da tawali'u da tausasawa ga ƙananan yara, da gyara zukatan manya ta hanyar girmama ƙananan yaransu da kuma zaunar da su a ƙirji, da makamancin haka.
- Najasar fitsarin yaro ko da bai fara cin abinci daomin sha'awa ba.
- Aikin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ana kiransa yayyafi, kuma ya keɓanci ƙaramin yaro ne wanda bai fara cin abinci ba, amma mace to babu makawa sai an wanke fitsarinta koda ta kasance ƙarama ce.
- Bahayar yaro wanda yake cin abinci ta hanyar tsotson nonon mahaifiyarsa to babu makawa a cikin hakan sai an wanke kamar sauran najasa.
- Babu makawa a wankewar daga wani al'amari na ƙari akan sanya ruwan.
- Abin da ya fi yin gaggawa da tsaftace bigiren najasar; dan gaggawa a tsarkaka daga kabasin, kuma dan kada a manta.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· TSARKI
· FIƘHU DA USULU
· GUSAR DA NAJASA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله
Subhanallah - Tsarkin Allah