Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga aljanna
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga aljanna
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga aljanna
Bayanin hadisin: Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga aljanna
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zaburar da kwaɗaitarwa akan sallar sanyaya biyu ; su ne sallar asuba da la'asar, kuma Ya yi wa wanda ya yi su da haƙƙinsu na lokaci da jama'a da wanin haka albishir cewa sun zama sababi na shigarsa aljanna.
Koyarwar hadisin: Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga aljanna
- Falalar kulawa akan sallar asuba da la'asar; domin asuba tana kasancewa ne a lokacin daɗin bacci, la'asar kuma tana kasancewa ne lokacin shagaltuwar mutum da aikinsa, wanda ya kiyayesu ya kasance mafi cancanta ya kiyaye ragowar salloli.
- An ambaci sallar asuba da la'asar da sanyaya biyu; domin sallar asuba a cikinta akwai sanyin dare, sallar la'asar kuma a cikinta akwai sanyin rana, koda sun kasance a lokaci na zafin rana, saidai wannan lokacin ya fi saukin (zafi) kafin wannan lokacin, ko kuma ambatansu ya zama ta babin rinjayarwa kamar yadda ake cewa: Watanni biyu ga rana da wata.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· SALLAH
· FIƘHU DA USULU
· FALALAR SALLAH
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa