Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafart…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ يَقُمْ لَيْلَةَ الْقَدْرِ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ»
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labari game da falalar tsayuwar Lailatul kadari wacce take kasancewa a goman ƙarshe na Ramadan, cewa wanda ya yi ƙoƙarin yin sallah a cikinta da addu'a da karatun al-ƙur'ani da zikiri, yana mai imani da ita, da kuma abin da ya zo a falalarta, yana mai kwaɗayin sakamakon Allah - Maɗaukakin sarki - da aikinsa, ba don riya ko jiyarwa ba, to, za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · AZUMI · FIƘHU DA USULU · SALLAR NAFILA · TSAYUWAR DARE · GOMAN ƘARSHE TA RAMADAN