Lallai Allah da manzonSa - sun haramta saida giya, da mushe da alade da gumaka

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Lallai Allah da manzonSa - sun haramta saida giya, da mushe da alade da gumaka

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Lallai Allah da manzonSa - sun haramta saida giya, da m…

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ عَامَ الفَتْحِ وَهُوَ بِمَكَّةَ: «إِنَّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ حَرَّمَ بَيْعَ الخَمْرِ، وَالمَيْتَةِ وَالخِنْزِيرِ وَالأَصْنَامِ»، فَقِيلَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَرَأَيْتَ شُحُومَ المَيْتَةِ، فَإِنَّهَا يُطْلَى بِهَا السُّفُنُ، وَيُدْهَنُ بِهَا الجُلُودُ، وَيَسْتَصْبِحُ بِهَا النَّاسُ؟ فَقَالَ: «لاَ، هُوَ حَرَامٌ»، ثُمَّ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عِنْدَ ذَلِكَ: «قَاتَلَ اللَّهُ اليَهُودَ إِنَّ اللَّهَ لَمَّا حَرَّمَ شُحُومَهَا جَمَلُوهُ، ثُمَّ بَاعُوهُ، فَأَكَلُوا ثَمَنَهُ».

Bayanin hadisin: Lallai Allah da manzonSa - sun haramta saida giya, da m…

Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda ad shi - ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa a shekarar da aka buɗe Makka, alhali shi yana Makka: Lallai Allah da ManzonSa sun haramta saida giya da mushe da alade da gumaka, sai aka ce :

Ya Manzon Allah, shin ya halatta mu saida kitsen mushe? domin su ana shafe jiragen ruwa da su, kuma shafe fatu da su, kuma mutane suna kunna fitilunsu da su, sai ya ce: A'a, saida su haramun ne, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce a wannan lokacin:

Allah Ya halakar da Yahudawa kuma Ya la'ancesu; lallai Allah yayin da Ya haramta musu kitsen dabbobi sai suka narkasu, sannan suka saida mansu suka ci kuɗinsa.

Koyarwar hadisin: Lallai Allah da manzonSa - sun haramta saida giya, da m…

Rukunan : ABIBCICCIKA DA ABUBUWAN SHA · ABIN DA YA HALATTA DAGA CIKIN DABBOBI DA TSUNTSAYE · FIƘHU DA USULU

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah