wani mutum ya zo a lokacin Annabi- mai tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi- y…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > wani mutum ya zo a lokacin Annabi- mai tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi- y…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: wani mutum ya zo a lokacin Annabi- mai tsira da amincin…

عن جابِر بن عبد الله رضي الله عنهما قال: «جاء رجل والنبي صلى الله عليه وسلم يَخْطُبُ الناس يوم الجمعة، فقال: صليت يا فلان؟ قال: لا، قال: قم فاركع ركعتين، -وفي رواية: فصل ركعتين-».

Bayanin hadisin: wani mutum ya zo a lokacin Annabi- mai tsira da amincin…

Sulaiku algadafaniy ya shiga masallacin Annabi a lokacin annabi maitsira da amincin Allah yana yiwa mtane huduba, sai ya zauna don ya ji huduba, alhalin bai yi sallar gaisuwar masallaci ba, kodai saboda ya jahilci hukuncin ta ko kuma yana zaton sauraraon hudubar yafi muhimmanci, amma hakan bai hana annabi mai tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya tunatar da shi ba shagaltuwar sa da huduba bai hana shi ya tsaya ya sanar da shi ba, har magana ma yayi masa da cewa: shin kayi sallah ya kai wane a gefen masallaci kafin na ganka? sai ya ce: a`a sai ya ce : tashi kayi raka`a biyu a cikin riwayar muslim ya umarce shi da ya takaita raka`o`in ma`ana ya saukaka su, ya fadi hakan ne a cikin babban taro domin ya koyar da mutumin cikin lokacin bukata, kuma domin koyarwar ta zamo gamammiya abar yadawa tsakanin mahalarta masallacin. Duk wanda ya shiga masallaci alhalin mai huduba yana huduba to abin shar`antawa a gareshi shi ne yin salla. dalilin da yake nuni akan haka shi ne wannan hadisin, da kuma hadisin: ''Idan dayan ku yazo a ranar juma`a alhalin limami yana huduba, to lallai yayi raka`a guda biyu''. saboda haka imamun-nawawiy ya fada a cikin sharhin muslim a wurin fadar sa mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi: ''Idan dayanku yazo alhalin limami yana huduba to lallai yayi raka`o`i biyu ya kuma takaita a cikin su'' sai ya ce: wannan nassi ne da baya neman karin bayani, ba kuma na zaton wannan lafazin zai isa zuwa ga wani masani da ya tabbatar da ingancinsa sa`annan kuma ya saba masa.

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SALLAR JUMA'A · HUKUNCE-HUKUNCEN HUƊUBAR JUMA'A

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah