Na yi tafiya da Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma ya kasanc…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Na yi tafiya da Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma ya kasanc…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Na yi tafiya da Manzon Allah -tsira da amincin Allah su…

عن عبد الله بن عُمر رضي الله عنهما قال: «صحبت رسول الله صلى الله عليه وسلم فكان لا يزيد في السَّفَر على ركعتين، وأبا بكر وعُمر وعُثْمان كذلك».

Bayanin hadisin: Na yi tafiya da Manzon Allah -tsira da amincin Allah su…

Abdullahi Dan Umar yana fada mana shi yayi tafiye-tafiye da Manzon Allah tsira da amincin Allah, hakanan yayi tafiye-tafiye da Abubakar da Umar da Usman Allah ya yarda dasu, kuma dukkaninsu sun kasance suna yin kasaru a sallolinsu masu raka'oi hurhudu,kuma basu yin sunnonin Rawatib a halin balaguro, ya ambaci Abubakar da Umar da Usman ne don ya nuna hukuncin baa shafe shi bayan wafatin Annabi ba yana nan tabbatace ne. Ya halarta a cika salla a halin balaguro, sai dai kasaru din ya fi; saboda fadinsa Madaukaki: {Ba laifa akanku da ku yi kasarun sallolin ku} fadin ba laifi da ayar tayi ya nuna cewa sauki ne aka bayar ba wai wajabci bane, saboda asali game da sha'anin salla shi ne a cika ta. abin da yafi ga matafiyi shi ne kar ya bar yin kasaru, saboda koyi da Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, kuma don fita daga sabanin masu cewa yin kasaru tilas ne, kuma don kasancewar yin kasaru shi ne yafi gun malamai gaba daya.

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SALLAR MASU UZURI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah