Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sannan ya tafi, kamar ya bayar da sad…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sannan ya tafi, kamar ya bayar da sad…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sa…

Bayanin hadisin: Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sa…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da falalar gaggawar tafiya zuwa sallar Juma'a. Gaggawa tana farawa ne daga bullowar rana zuwa lokacin zuwan liman; shi ne sa'o'i biyar, ana karkasasu kaso biyar gwargwadan lokaci tsakanin bullowar rana har zuwa shigowar liman da hawansa minbari dan huɗuba:

Na farko: Wanda ya yi wanka cikakke kamar wankan janaba, sannan ya tafi masallacin Juma'a a lokaci na farko kamar ya yi sadaka da taguwa ne.

Na biyu: Wanda ya tafi a lokaci na biyu kamar ya yi sadaka da saniya ne.

Na uku; Wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya yi sadaka ne da rago - shi ne namijin tinkiya - mai ƙahuhhuna.

Na huɗu: Wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya yi sadaka ne da kaza.

Na biyar: Wanda ya tafi a lokaci na biyar kamar ya yi sadaka ne da ƙwai.

Idan liman ya fito dan huɗuba; sai mala'ikun da suke zaune a ƙofofi dan rubuta masu shiga masallaci na farko da mai biye da shi sai su dakatar da rubutu, sai su zo suna jin zikiri da huɗuba.

Koyarwar hadisin: Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sa…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · TSARKI · SALLAH · FIƘHU DA USULU · WANKA · SUNNONI DA LADUBBAN WANKA · SALLAR JUMA'A

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah