Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Duk wanda ya yi sallah kafin ɓullowar rana da kafin faɗuwarta ba zai shiga wuta ba
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Babu wani ɗaya wanda ya sallaci sallar Asuba, da sallar La'asar kuma ya dawwama a kansu da zai shiga wuta; ya keɓanci waɗannan salloli biyun; domin cewa su ne mafi nauyin salloli, kuma cewa lokacin safiya yana kasancewa ne lokacin bacci da daɗinsa, lokacin La'asar kuma yana kasancewa ne a lokacin shagaltuwa da ayyukan yini da kuma kasuwancinsa, wanda ya kiyaye akan waɗannan salloli biyun tare da samun wahala to zai kiyaye akan ragowar sallolin.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · FALALAR SALLAH