Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsinewa mai karɓar rashaw…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsinewa mai karɓar rashaw…
Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare…
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: لَعَنَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الرَّاشِيَ وَالْمُرْتَشِيَ فِي الْحُكْمِ.
Bayanin hadisin: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mummnar addu'a da korewa da nisantarwa daga rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - a kan mai ba da rashawa da mai karɓarta.
Daga hakan akwai abin da ake ba wa alƙalai don su yi zalunci a hukuncin da suke jiɓintarsa; don mai bayarwa ya kai ga manufarsa ba tare da wani haƙƙi ba.
Koyarwar hadisin: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare…
- Ba da rashawa yana haramta, da karɓarta da yin hanya zuwa gareta, da taimako a kanta; don abin da ke cikinta na taimakekeniya a kan ƙarya (ɓarna).
- Rashawa tana daga manyan zunubai; domin cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsinewa mai karɓarta da mai ba da ita.
- Rashawa a shari'a (Alƙalanci) da hukunci ita ce mafi girman laifi, kuma mafi tsanani; don abin da ke cikinta na zalunci da hukunci ba tare da abin da Allah Ya saukar ba.
Rukunan :
ALƘALANCI
· LADUBBAN ALƘALI
· FIƘHU DA USULU
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad