Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son (shiga) Musulu…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son (shiga) Musulu…
Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata…
عن قيس بن عاصم رضي الله عنه قال: أتيتُ النبيَّ صلى الله عليه وسلم أُريدُ الإسلامَ، فأَمَرَني أن أغتَسِلَ بماءٍ وسِدرٍ.
Bayanin hadisin: Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata…
Ƙais ɗan Asim ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - alhali yana son ya musulunta, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce shi ya yi wanka da ruwa da (ganyan) bishiyar magarya; don kasancewa ganyanta ana amfani da shi a tsafta; don kuma abin da take da shi na ƙamshi mai daɗi.
Koyarwar hadisin: Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata…
- Halaccin wankan kafiri a lokacin shigarsa Musulunci.
- Darajar Musulunci da kulawarsa da jiki da rai gabaɗaya.
- Cakuɗa ruwa da abubuwa masu tsarki ba ya fitar da shi daga tsarki.
- Abubuwa na tsafta na zamani suna tsayawa a matsayin magarya, kamar sabulu da makamantansa.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· TSARKI
· FIƘHU DA USULU
· WANKA
· ABUBUWAN DA SUKE WAJABTA WANKA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa