Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tu…
Bayanin hadisin: Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tu…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayya cewa wanda ya mance yin kowacce sallar farilla har lokacinta ya fita, to, ya wajaba a kansa ya yi gaggawar ramata a duk lokacin da ya tunata, babu gogewa ko suturtawa ga laifin barinta sai dai kawai musulmi ya sallaceta a yayin da ya tunata, Allah Ya faɗa a littafinSa Mai girma: {Ka tsai da sallah domin tunaNi} [Daha: 14], wato: Ka tsai da sallar daka manta idan ka tunata.
Koyarwar hadisin: Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tu…
- Bayanin muhimmancin sallah da rashin ko’unkula da yinta da kuma ramata.
- Jinkirta sallah daga lokacinta da gangan ba tare da wani uzuri ba ba ya halatta.
- Wajabcin rama sallah a kan mai mantuwa idan ya tuna, da mai bacci idan ya farka.
- Wajabcin rama salloli a gaggauce ko da a lokutan hani ne.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· SALLAH
· FIƘHU DA USULU
· WAJIBCIN SALLAH DA HUKUNCIN MAI BARINTA
· KURAKUREN MASU SALLAH
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله
Subhanallah - Tsarkin Allah