An sa mana lokaci a rage gashin baki, da yanke farata, da cire gashin hammata, da aske gas…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > An sa mana lokaci a rage gashin baki, da yanke farata, da cire gashin hammata, da aske gas…
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: An sa mana lokaci a rage gashin baki, da yanke farata,…
Bayanin hadisin: An sa mana lokaci a rage gashin baki, da yanke farata,…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iyakance akan rage gashin bakin namiji, da yanke farcen hannaye da ƙafafuwa, da cire gashin hammata, da aske gashin mara, cewa kada a barsu sama da kwanaki arba'in.
Koyarwar hadisin: An sa mana lokaci a rage gashin baki, da yanke farata,…
- Shaukani ya ce: Abin aka fi so shi ne a iyakance kwana arba'in waɗanda manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iyakance su dan haka ba ya halatta a ƙetaresu, wanda ya bar askewar da makamncinsa bayan tsawo har zuwa ƙarshen waccan lokacin na kwanaki arba’in to ba za'a ƙirga shi cikin wanda ya saɓawa sunnah ba.
- Ibnu Hubaira ya ce: Wannan hadisin shi ne matuƙa a jinkirta hakan, abinda ya fi a yi riƙo da ƙasa da wannan matuƙar.
- Kulawar musulunci da tsafta da tsarkaka da kuma ado.
- Rage gashin baki, shi ne a rage wasu daga gashin da ya tsiro akan leɓe na sama.
- Cire gashin hammata, yana kasancewa ne da kawar da gashin da yake tsirowa da shi, shi ne gurin da yake kasancewa ƙasan mararrabar zira'i da kafaɗa.
- Aske gashin mara, shi ne gashi mai kaushi wanda ya tsiro a gefen gaba daga namiji da mace.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· TSARKI
· FIƘHU DA USULU
· SUNNONIN FITRA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا إله إلا الله
Babu abin bautawa sai Allah