Cewa wani mutum ya yi alwala, sai ya bar tabo (Lam’a) gurin farce a kan ƙafafunsa, sai Ann…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Cewa wani mutum ya yi alwala, sai ya bar tabo (Lam’a) gurin farce a kan ƙafafunsa, sai Ann…
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne a baki dayan ruwayoyin sa
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Cewa wani mutum ya yi alwala, sai ya bar tabo (Lam’a) g…
عَنْ جَابِرٍ رضي الله عنه قال: أَخْبَرَنِي عُمَرُ بْنُ الْخَطَّابِ: أَنَّ رَجُلًا تَوَضَّأَ فَتَرَكَ مَوْضِعَ ظُفُرٍ عَلَى قَدَمِهِ فَأَبْصَرَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: «ارْجِعْ فَأَحْسِنْ وُضُوءَكَ» فَرَجَعَ، ثُمَّ صَلَّى.
Bayanin hadisin: Cewa wani mutum ya yi alwala, sai ya bar tabo (Lam’a) g…
Umar - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum ya gama alwalarsa, sai ya bar gwargwadan farce a ƙafarsa (Lam’a) ruwa bai same shi ba, sai ya ce masa yana mai nuni zuwa gurin da bai sami ruwa ba: Ka koma ka kyautata alwalarka ka cikata ka ba wa kowacce gaba haƙƙinta na ruwa. Sai mutumin ya koma ya cika alwalarsa, sannan ya yi sallah.
Koyarwar hadisin: Cewa wani mutum ya yi alwala, sai ya bar tabo (Lam’a) g…
- Wajabcin gaggawa zuwa horo da aikin alheri, da fadakar da wanda bai sani ba da rafkananne, musamman ma idan barnar ta kasance lalacewar ibadarsa za ta kasance akan akan barnar.
- Wajabcin game gabban alwala da ruwa, kuma cewa wanda ya bar wani yanki daga gaba - koda ƙarami ne - alwala ba ta ingantuwa daga gare shi, kuma sakewa ce ta wajaba idan ya jima kafin ya gani.
- Halaccin kyautata alwala, hakan ta hanyar cikata da kyautata akan yadda aka yi umarni da ita a shari'ance.
- Kafafuwa biyu suna daga gabban alwala, kuma shafa ba ta isuwa a cikinsu, kawai babu makawa sai an wanke su.
- Jerantawa, yana kamata tsakanin gabban alwala, ta yadda zai wanke kowacce gaba kafin ta gabaninta ta bushe.
- Rashin sani da mantuwa ba sa sarayar da wajibi, kawai suna sarayar da zunubi ne, wannan mutumin wanda bai kyautata alwalarsa ba saboda rashin sani, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi bai sarayar masa da wajibi ba, wato alwala, kawai ya umarce shi ya saketa.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· TSARKI
· FIƘHU DA USULU
· ALWALA
· RUKUNAN ALWALA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
أستغفر الله
Ina neman gafara daga Allah