Idan ɗayanku ya yi kokwanto a cikin sallarsa, bai san nawa ya sallata ba shin uku ne ko hu…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Idan ɗayanku ya yi kokwanto a cikin sallarsa, bai san nawa ya sallata ba shin uku ne ko hu…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Idan ɗayanku ya yi kokwanto a cikin sallarsa, bai san n…

Bayanin hadisin: Idan ɗayanku ya yi kokwanto a cikin sallarsa, bai san n…

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mai sallah idan ya yi taraddudi a cikin sallarsa bai san nawa ya sallata ba, shin uku ne ko huɗu? to ya nisantar da adadin da ya yi kokwanto cikinsa kada ya yi anfani da shi; ukun su ne abin da aka yi yaƙini akan su, sai ya sallaci raka'a ta huɗu, sannan sai ya yi sujjada kafin ya yi sallama.

Idan abinda ya sallata huɗu ne a haƙiƙa; to sun zama biyar in an kara raka'ar, sajadodi biyun na rafkanuwa canji ne ga raka'a, sai adadin ya zama biyu kenan ba ɗaya ba, idan kuma ya sallaci huɗu ne da wannan raka'ar ta ƙari; sai ya zama ya bada abinda ke kansa ba tare da ƙari ko ragi ba.

Sujjada biyun na rafkanuwa sun zama ƙasƙantarwa ga Shaiɗan da kuma halakarwa gare shi, da dawo da shi a taɓe abin nisantarwa daga manufarsa; domin shi ya cakuɗa masa sallarsa, ya bijiro dan ɓata ta, kuma sallar ɗan Adam ta cika yayin da ya yi riko da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki - da yin sujjadar da Iblis ya saɓa maSa da ita, lokacin da ya ki biyayya ga Allah da yin sujjada ga (Annabi) Adam.

Koyarwar hadisin: Idan ɗayanku ya yi kokwanto a cikin sallarsa, bai san n…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SUJJADAR RAFKANUWA DA TILAWA DA GODIYA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah