Manzo tsira da amincin Allah sun shiga gida, da Usama Dan Zaidu da Bilal da Usman Dan Dalh…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Manzo tsira da amincin Allah sun shiga gida, da Usama Dan Zaidu da Bilal da Usman Dan Dalh…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Manzo tsira da amincin Allah sun shiga gida, da Usama D…

عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال: «دخل رسول الله صلى الله عليه وسلم البيت، وأسامة بن زيد وبلال وعثمان بن طلحة، فأغلقوا عليهم الباب فلما فتحوا كنت أولَ من وَلَجَ. فلقيتُ بلالًا، فسألته: هل صلى فيه رسول الله صلى الله عليه وسلم ؟ قال: نعم ، بين العَمُودَيْنِ اليَمَانِيَيْنِ».

Bayanin hadisin: Manzo tsira da amincin Allah sun shiga gida, da Usama D…

Lokacin da Allah madaukaki ya bude makha, ya tsarkake dakinsa daga gumaka da butunbutumai da hotuna, sai tsira da aminci ya shiga Dakin Ka'abaa madaukakiya, a tare da shi akwai mai yi masa hidima, Bilal da Usama,da mai kula da gida Usman Dan Dalha,sai aka kulle musu kofa don kada mutane su yi cincirindo wajen shigowar Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi,don su ga ydda yake yin bauta, gudun kar su shagaltar da shi daga abin da yake son yi a wajen,shi ne ganawa da Ubangijinsa tare da gode masa bisa ni'imominsa, yayin da suka jima suna jira , sai aka bude kofar.Abdullahi Dan Umar ya kasance mai tsananin kwadayin bibiyar Sunnar Annabi ne don haka ya zama farkon wanda ya shiga bayan an bude kofar.Sai ya tambayi Bilal : shin Annabi ya yi salla anan ciki ne? sai Boilal yace: e, ya yi salla a tsakanin ginshikan can na bangaren dama .a lokacin Ka'aba Mai tsarki tana da ginshikai shida ne,sai ya sanya uku a bayansa,biyu a damansa daya kuma a hagunsa, kuma ya bar tazara kamu uku tsakaninsa da katanga, sai sallaci raka'a biyu, kuma ya yi addu'a abangarori hudu.

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SHARUƊAN SALLAH

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah