An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har saida ya wayi gari a wurin Annabi - tsi…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har saida ya wayi gari a wurin Annabi - tsi…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har said…
Bayanin hadisin: An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har said…
An anbaci wani mutumin da ya yi bacci har gari ya waye rana ta ɓullo bai tashi ya yi sallar farilla ba a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai shi wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnansa.
Koyarwar hadisin: An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har said…
- Karhancin barin tsayuwar dare, kuma cewa hakan da sababin Shaiɗan ne.
- Tsoratarwa daga Shaiɗan wanda yake zama ga mutum a kan kowace hanya; dan ya tsare tsakaninsa da tsakanin ɗa'ar Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
- Ibnu Hajar ya ce: Faɗinsa: (Bai tashi zuwa sallah ba) abin nufi jinsi, kuma zai iya ɗaukar alƙawari, kuma ana nufin sallar dare ko (sallar) farillah da shi.
- Al-Ɗaibi ya ce: An keɓanci kunne da anbato, duk da ido yafi dacewa da bacci, dan yin nuni zuwa nauyin bacci, domin cewa kunnuwa sune magangarar farkawa, kuma an keɓanci fitsari; domin cewa shi ya fi sauƙin shiga a cikin ciki, kuma mafi saurin zarcewa a cikin jijiyoyi, sai ya gadar da kasala a cikin dukkan gaɓɓai.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· SALLAH
· FIƘHU DA USULU
· WAJIBCIN SALLAH DA HUKUNCIN MAI BARINTA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الحمد لله
Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah