Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi ne za su shiga ta c…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi ne za su shiga ta c…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayy…
Bayanin hadisin: Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayy…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai wata ƙofa daga cikin ƙofofin aljanna ana kiranta: Kofar Rayyan, masu azimi zasu shigeta ranar alƙiyama, babu wanda zai shiga (aljanna) ta kofar sai su, za’a yi kira: Ina masu azimi, sai su miƙe su shiga, waninsu ba zai shiga ba, idan na ƙarshensu ya shiga sai akulleta, babu wani da zai shiga bayan nan.
Koyarwar hadisin: Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayy…
- Nawawi ya ce: A cikin hadisin akwai falalar azimi da kuma girman masu azimin.
- Allah Ya ware wata ƙofa daga cikin ƙofofin aljanna guda takwas ga masu azimi, idan suka shiga ta kofar sai akulleta.
- Bayanin cewa aljanna tana da ƙofofi.
- Sindi ya ce: Faɗinsa: (Ina masu azimi), wato masu yawaita yin azimi kamar mai adalci da azzalimi, ana faɗin haka ga wanda ya saba da hakan, ba ga wanda ya aikata sau ɗaya ba kawai.
- (al-Rayyan) yana nufin wacce take ƙosarwa; domin cewa masu azimi suna jin ƙishirwa musammanma dai acikin kwanukan bazara masu tsawo masu zafi; sai a yi musu sakayya da ambatan wannan ƙofar da abinda yake keɓantarsu da shi da sunan ƙofar Arrayyan, kuma an ce Arrayyan wato Fa'alan mai yawan ƙoshi kishiyar ƙishirwa, an anbaceta da shi; domin cewa ita sakamakon masu azimi ce saboda ƙishirwarsu da kuma yunwarsu.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· AZUMI
· FIƘHU DA USULU
· FALALAR AZUMI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
أستغفر الله
Ina neman gafara daga Allah