Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin sahur
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin sahur
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin…
Bayanin hadisin: Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan sahur shi ne cin (abin ci) a ƙarshen dare dan yin tanadi ga azimi; domin cewa a cikinsa akwai (albarka) alheri mai yawa na lada da sakamako, da tashi a ƙarshen dare dan addu'a, da ƙarfafuwa akan azimi, da nishaɗuwa gare shi, da kuma sauƙaƙa wahalarsa.
Koyarwar hadisin: Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin…
- An so sahur da riko umarnin shari'a da aikata shi.
- Ibnu Hajar ya ce a cikn Fathul Bari: Albarka a cikin sahur tana samuwa ne ta ɓangarori masu yawa, su ne bin sunna, da saɓawa Ahlul kitabi, da ƙarfafuwa da shi akan ibada, da ƙari a cikin nishaɗi, da tunkuɗe munanan ɗabi'u wanda yunwa take taso shi, da kawo sababin sadaka ga wanda yake roƙo a wannan lokacin ko yake haɗuwa da shi akan cin abin ci, da sabbaba zikiri da addu'a a lokacin ana fatan amsawa, da riskar niyyar azimi ga wanda ya rafkana daga gareta kafin ya yi bacci.
- Kyakkyawar koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda yake haɗa hukunci da hikima; dan ƙirji ya buɗe da shi, kuma a san matsayin shari'a da shi.
- Ibnu Hajar ya ce: Sahur yana samuwa ne da mafi ƙarancin abinda mutum yake samunsa na abin ci da abin sha.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· AZUMI
· FIƘHU DA USULU
· SUNNONIN AZUMI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
أستغفر الله
Ina neman gafara daga Allah