Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Babu Zakka a kasa da Ukiyya Biyar , ko kuma kasa da Rakuma Biyar, ko kasa da Buhu biyar.
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أبي سعيد الْخُدْرِي رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «ليس فيما دون خمس أَوَاقٍ صدقة، ولا فيما دون خمس ذَوْدٍ صدقة، ولا فيما دُونَ خمسة أَوْسُقٍ صدقة».
Zakka: Yalwatawa ce tsakanin Mawadata da Mabukata, Kuma don haka ne ma ba'a karba daga wanda kudinsa basu taka kara sun karya ba don ba'a daukarsa Mawadaci.To kuma Sharia ta bayyana Mafi karancin abinda ya Wajaba ayi Zakka a kansa, amma kuma Duk wanda ya Mallaki kasa da Mafi karancin Haddin Zakka, to cewa shi Mabukaci ba'a karbar komai daga Wurinsa, to Ma'abocin Azurfa, Bai wajaba akansa Zakka har Sai ya kasance yana da Ukiyya biyar, kuma Ukiyya ita ce Dirhami Arba'in, to sai ya kasance Nisabin Zakkarsa a ciki Dirhami Dari biyu, wanda yayi daidai da Gram Dari biyar da Casa'in, kuma Mai zakkar Rakumabata wajaba akansa ba, har sai yana da Rakuma Biyar ko sama da haka, kuma kasa da haka babu zakka a ciki. kuma Mai Zakkar kayan Gonababu zakka a kansa sai ta kai Buhu biyar, kuma Buhu shi ne kwano Sittin, to sai ya kasance Nisabinsa shi Kwano Dari Uku.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · ZAKKA · FIƘHU DA USULU · ZAKKAR KUƊI · ZAKKAR DABBOBIN GIDA · ZAKKAR ABIN DA GONA TA FITAR