Idan dayanku ya yi alwala kuma ya sanya huffinsa to ya yi sallah da su, kuma ya yi shafa a…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Idan dayanku ya yi alwala kuma ya sanya huffinsa to ya yi sallah da su, kuma ya yi shafa a…
Wanda ya ruwaito hadisin: Dar Al-Kutni ne Ya Rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Idan dayanku ya yi alwala kuma ya sanya huffinsa to ya…
Bayanin hadisin: Idan dayanku ya yi alwala kuma ya sanya huffinsa to ya…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa idan musulmi ya sanya huffinsa bayan ya yi alwala, sannan ya kari (hadasi) bayan nan kuma ya yi nufin alwala, to yana da damar yin shafa akansu idan ya yi nufin hakan, kuma ya yi sallah da su kada ya ciresu a wani sanannen lokaci, sai dai idan ya samu janaba to cire huffin ya wajaba a gare shi saboda yin wanka.
Koyarwar hadisin: Idan dayanku ya yi alwala kuma ya sanya huffinsa to ya…
- Shafa akan huffi ba ta halatta sai dai idan an sanya huffin bayan cikar alwala.
- Tsawan lokacin shafa ga mazauni: Shafa yini da dare, matafiyi kuma: Yini uku da dararensu.
- Shafa akan huffi yana keɓantar ƙaramin hadasi ne banda babba, amma hadasi babba to shafa tare da shi ba ya halatta, kai babu makawa sai an cire huffin da kuma wanke ƙafafuwan.
- An so yin sallah da takalmi da kuma huffi da makancinsu dan saɓawa Yahudawa, hakan idan sun kasance masu tsarki, kuma babu cutar da masu yin sallah da su, ko (cutar da) masallaci kamar masallacin da aka shinfiɗa masa shinfiɗu to ba za’a yi sallah da su ba.
- Akwai sauƙi da sawwaƙawa ga wannan al'ummar a (lamarin) shafa akan huffi.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· TSARKI
· FIƘHU DA USULU
· SHAFA A KAN HUFFI DA MAKAMANTANSA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad