Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga…
Musulunci > Ha > Hadith > Falalar sahabbai > Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma ba…
Bayanin hadisin: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma ba…
Sarkin muminai Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya zo wajen Hajarul Aswad a kusurwar Ka'aba sai ya sunbace shi, sai ya ce: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.
Koyarwar hadisin: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma ba…
- Halaccin sunbatar Hajarul Aswad ga masu ɗawafi lokacin da suka yi daura da shi, idan zai yi wu kuma cikin sauƙi.
- Abin nufi daga sunbatar Hajaraul Aswad, shi ne bin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Nawawi ya ce: Ma'anarsa cewa babu wani iko gare shi akan anfanarwa ko cutarwa, kuma cewa shi dutse ne abin halitta kamar ragowar halittun da basa cutarwa kuma basa anfanarwa, kuma (sayyadina) Umar ya yaɗa wannan ne a lokacin Mausim (Hajji); dan ya shaida waa kasashe, kuma ma'abota Mausim (Hajji) mabanbantan ƙasashe su kiyaye.
- Ibadu a tsaye suke (ababen shara'antawa ne daga Allah da ManzonSa kadai); ba'a shara'anta wani abu na ibada sai abinda Allah da ManzonSa suka shara'anta.
- Idan ibada ta inganta za’a yi aiki da ita koda ba'asan hikimarta ba; domin cewa rikon da mutane suka yi da umarni da kuma biyayyarsu a kan tsayuwa da ita yana daga hikimomi ababen nufi.
- Hani daga sunbatar abinda shari'a ba ta zo da sunbatarsa ba ta hanyar bauta na duwatsu da wasunsu.
Rukunan :
FALALAR SAHABBAI
· FIƘHU NA IBADA
· HAJJI DA UMRA
· ILIMIN AƘIDA
· FIƘHU DA USULU
· HUKUNCE-HUKUNCE DA MAS'ALOLIN HAJJI DA UMRA
· SAHABBAI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله
Subhanallah - Tsarkin Allah