Na ga Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi lokacin da yazo Makka in ya sumba…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Na ga Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi lokacin da yazo Makka in ya sumba…

Wanda ya ruwaito hadisin: Buhari da Muslim suka rawaito shi da ruwayoyin sa

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Na ga Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare sh…

عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال: « تَمَتَّعَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم فِي حَجَّةِ الوَدَاع بالعُمرَة إلى الحج وأهدَى، فَسَاقَ مَعَهُ الهَدْيَ مِن ذِي الحُلَيفَة، وَبَدَأَ رَسول اللَّهِ صلى الله عليه وسلم وَأَهَلَّ بالعمرة، ثُمَّ أَهَلَّ بالحج، فَتَمَتَّعَ النَّاس مع رسول اللَّهِ صلى الله عليه وسلم فَأَهَلَّ بالعمرة إلَى الحج، فَكَان مِن النَّاس مَنْ أَهْدَى، فَسَاقَ الهَدْيَ مِن ذي الحُلَيفَة، وَمِنهُم مَنْ لَمْ يُهْدِ، فَلَمَّا قَدِمَ رسول اللَّه صلى الله عليه وسلم قَالَ للنَّاس: مَنْ كَانَ مِنكُم أَهْدَى، فَإِنَّهُ لا يَحِلُّ مِن شَيء حَرُمَ مِنْهُ حَتَّى يَقْضِيَ حَجَّهُ، وَمَن لَم يَكُن أَهْدَى فَلْيَطُفْ بالبَيت وَبالصَّفَا وَالمَروَة، وَلْيُقَصِّر وَلْيَحْلِل، ثُمَّ لِيُهِلَّ بالحج وليُهدِ، فَمَن لم يجد هَدْياً فَلْيَصُم ثَلاثَةَ أَيَّام فِي الحج وَسَبعة إذَا رَجَعَ إلى أَهلِهِ فَطَافَ رسول اللَّهِ صلى الله عليه وسلم حِينَ قَدِمَ مَكَّةَ، وَاستَلَمَ الرُّكْنَ أَوَّلَ شَيْءٍ، ثُمَّ خَبَّ ثَلاثَةَ أَطْوَافٍ مِنْ السَّبْعِ، وَمَشَى أَربَعَة، وَرَكَعَ حِينَ قَضَى طَوَافَهُ بالبيت عِند المَقَام رَكعَتَين، ثُمَّ انصَرَفَ فَأَتَى الصَّفَا، وطاف بِالصَّفَا وَالمَروَة سَبعَةَ أَطوَاف، ثُمَّ لَم يَحلِل مِنْ شَيْءٍ حَرُمَ منه حَتَّى قَضَى حَجَّهُ، وَنَحَرَ هَدْيَهُ يوم النَّحرِ، وَأَفَاضَ فَطَافَ بالبيت، ثُمَّ حَلَّ مِن كُلِّ شَيء حَرُمَ مِنهُ، وَفَعَلَ مِثل مَا فَعَلَ رَسول اللَّه صلى الله عليه وسلم : مَن أَهدَى وَسَاقَ الهَديَ مِن النَّاسِ».
«رَأَيْتُ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم حِينَ يَقْدَمُ مكَّة إذا اسْتَلَمَ الرُّكْنَ الأَسْوَدَ -أَول ما يَطُوفُ- يَخُبُّ ثَلاثَةَ أَشْوَاطٍ».

Bayanin hadisin: Na ga Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare sh…

Yayin da Annabi -tsira da amincin Allah- ya fita izuwa Zulhulaifa " Mikatin Mutanen Madina" don yin Hajjinsa ta bankwana, yayi bankwana da Dakin Allah yayi bankwana da mutane, yayi bankwana da Aikin hajjin, kuma ya shaidar da cewa ya isar da sakon Allah zuwa ga mutane, sai ya daura haramin yin umara da hajji, sai yayi kirani, Kirani shi ne Tamattu'i, sai mutane suka yi tamattu'i tare da Manzo tsira da aminci su tabbata a gare shi- wasu suka yi haramar yin umra da hajji gaba daya, wasu kuma suka yi haramar yin umara, tare da niyyar yin hajji bayan sun gama umra, wasu kuma suka yi niyyar yin hajji kadai,Annabi -tsira da amincin Allah ya basu zabi tsakanin abu ukun, Annabi tsira da aminci da wasu daga sahabbai suka taho da hadayarsu daga Zulhulaifa, wasu kuma basu taho da ita ba, yayin da suka kusa da Makka sai Annabi tsira da amincin Allah ya kwadaitar da wadanda suke ifradi da masu kirani amma basu taho da hadaya ba su mayar da niyyarsu ta yin umara, bayan sunyi dawafi da saayi sai yace su yi saisaye, su warware umararsu sannan suyi harramar hajji kuma suyi hadaya, saboda yin umara da hajji a tafiya daya, wanda kuma bashi da hadaya, to yayi azumi goma, uku a can bakwai kuma in ya koma garinsu.Lokacin da Annabi tsira da amincin Allah yazo Makka sai ya sumbaci Rukni, yayi dawafi bakwai, yayi uku da sauri kasancewar sune na farko bayan zuwansa, yayi hudu a hankali, sannan yayi salla raka'a biyu a Makamu Ibrahim, sannan yayi Safa da Marwa sau bakwai, yana yin sassarfa a tsakanin alamomi biyu, yayi tafiya a inda ba nan ba, kuma bai kwance haraminsa ba har sai da ya gama hajji, ya soke hadayarsa ranar sokewa, bayan ya gama hajjinsa ya jefi Jamrat Al'akba, ya soke hadayarsa, ya aske kansa. Wannan shine tahalluli na farko, sai yayi dawafin ifadwa, sannan ya halarta komai, harma da kusantar iyali, duk sahabban da suka zo da hadaya suma suka yi haka.

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · HAJJI DA UMRA · FIƘHU DA USULU · SIFFAR AIKIN HAJJI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله Subhanallah - Tsarkin Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah