Shi ruwansa mai tsarkakewa ne, kuma mushensa halal ne

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Shi ruwansa mai tsarkakewa ne, kuma mushensa halal ne

Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Shi ruwansa mai tsarkakewa ne, kuma mushensa halal ne

Bayanin hadisin: Shi ruwansa mai tsarkakewa ne, kuma mushensa halal ne

Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Lallai mu muna hawa jiragen ruwa a cikin kogi dan sū ko kasuwanci da abinda ya yi kama da hakan, kuma muna ɗaukar ruwa kaɗan wanda za'a iya sha, idan muka yi anfani da ruwan shan dan yin alwala da wanka zai ƙare, kuma ba zamu samu wanda zamu sha ba, shin ya halatta garemu mu yi alwala da ruwan kogi?

Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce game da ruwan kogi: Ruwansa mai tsarki ne kuma mai tsarkakewa; alwala tana halatta da shi da kuma wanka da shi, kuma halal ne cin abinda yake fita daga cikinsa na kifaye da wasunsu, koda an samu mushe ya fito a bayansa ba tare da an yi sū dinsa ba.

Koyarwar hadisin: Shi ruwansa mai tsarkakewa ne, kuma mushensa halal ne

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · TSARKI · FIƘHU DA USULU · HUKUNCE-HUKUNCEN RUWA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah