Wasu jama'a daga al'ummata ba za su gushe ba suna masu rinjaye, har sai al'marin Allah ya …
Musulunci > Ha > Hadith > Characteristics of the people of the sunnah and the community > Wasu jama'a daga al'ummata ba za su gushe ba suna masu rinjaye, har sai al'marin Allah ya …
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wasu jama'a daga al'ummata ba za su gushe ba suna masu…
Bayanin hadisin: Wasu jama'a daga al'ummata ba za su gushe ba suna masu…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu mutane ba za su taɓa gushewa ba daga al'ummata suna masu rinjaye akan mutane, masu rinjayar waɗanda suka saɓa musu, hakan har sai al'amarin Allah ya zo musu ta hanyar karɓar rayukansu a ƙarshen zamanin duniya kafin tashin alƙiyama.
Koyarwar hadisin: Wasu jama'a daga al'ummata ba za su gushe ba suna masu…
- Mu'ujiza bayyananniya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, domin cewa wannan siffar bata gushe ba da godiyar Allah tun daga zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - har zuwa yanzu, kuma (wannan siffar) ba za ta gushe ba har sai al'amarin Allah ya zo wanda aka ambata a cikin hadisin.
- Falalar tabbata akan gaskiya da kuma aiki da ita, da kwaɗaitarwa akan hakan.
- Rinjayar Addini nau'i biyu ne: Kodai rinjaye da hujja da kuma bayani da bayyana, ko rinjaye da ƙarfi da kuma makami, kuma rinjayen mai wanzuwa ne da hujja da kuma bayani; domin cewa hujjar Musulunci ita ce Alƙur'ani, shi mai rinjaye ne kuma mai nasara ne akan maƙiyansa, sai dai nau'i na biyu na rinjaye, shi ne rinjayen ƙarfi da makami to wannan da gwargwadan imani ne da kuma tabbata a cikin ƙasa.
Rukunan :
Characteristics of the People of the Sunnah and the Community
· ILIMIN AƘIDA
· People of the Sunnah and the Community
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
أستغفر الله
Ina neman gafara daga Allah