Mata biyu sun yi fada daga Huzail.Sai daya daga cikinsu ta jefi daya da Dutse,sai ta kashe…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Mata biyu sun yi fada daga Huzail.Sai daya daga cikinsu ta jefi daya da Dutse,sai ta kashe…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Mata biyu sun yi fada daga Huzail.Sai daya daga cikinsu…

عن أبي هُرَيْرة رضي الله عنه قال: «اقْتَتَلَتْ امْرَأَتَانِ مِنْ هُذَيْلٍ، فرمَت إحداهما الأخرى بحجر، فَقَتَلَتْهَا وَمَا فِي بَطْنِهَا فَاخْتَصَمُوا إلَى النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم فَقَضَى رسول الله: أَنَّ دِيَةَ جَنِينِهَا غُرَّةٌ- عَبْدٌ، أَوْ وَلِيدَةٌ- وَقَضَى بِدِيَةِ المرأة على عَاقِلَتِهَا، وَوَرَّثَهَا وَلَدَهَا وَمَنْ مَعَهُمْ، فَقَامَ حَمَلُ بنُ النَّابِغَةِ الهُذَلِيُّ، فَقَالَ: يا رسول الله، كيف أغرم من لا شَرِبَ وَلا أَكَلَ، وَلا نَطَقَ وَلا اسْتَهَلَّ، فَمِثْلُ ذَلِكَ يُطَلُّ؟ فقال رَسول الله صلى الله عليه وسلم : «إنما هذا من إخوان الكُهَّان» من أجْل سَجْعِهِ الَّذِي سَجَعَ.

Bayanin hadisin: Mata biyu sun yi fada daga Huzail.Sai daya daga cikinsu…

Mata biyu sun yi Husuma daga Kabilar Huzail,sai Daya daga cikinsu ta jefi Daya da Dutse Karami,wanda galibi baya kisa,saidai cewa shi ya kasheta ya kuma kashe Tayinta da yake cikinta.Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi Hukunci da cewa Diyyar Dan Tayin,Bawa ko Baiwa,dai-dai ne Dan tayin Namiji ne ko Mace,kuma Diyyarsa tana kan wacce tayi kisan.Kuma yayi Hukunci ga Matar da aka kashe da Diyya,domin kisan nata kisa ne mai kama da ganganci,kuma yana kan Yan-uwar Matar,domin an gina tane abisa Taimakekeniya da Adalci,kuma saboda kisan bana ganganci bane.Kuma domin cewa Diyya gado ce ta wacce aka kashe saboda haka Danta da wadanda suke tare dashi a Magada sune zasu karbeta,sauran Yan-uwa basu da komai daga gareshi.Sai Hamalu Dan Al-Nabiga-shine Mahaifin wacce tayi kisan- yace:Ya Ma'aikin Allah,yaya zamu biya wanda akai barinsa amace,bai taba ci ba ,bai taba sha ba,bai taba magana ba,har agane rayuwarsa da hakan?ya fadi hakan da Usulubin Zance abin yiwa saja'i.Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya kyamaci Maganar tasa,saboda abin dake cikinta na raddin hukunce-hukuncen shari'a da irin wannan saja'oin dorawa kai masu kama da saja'oin Bokaye wadanda suke cin Dukiyoyin Mutane da ita bada .Gaskiyaba

Rukunan : LAIFUFFUKA NA ZUBAR DA JINI · DIYYA · FIƘHU DA USULU

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah