Idan kare ya sha a kwaryar ɗayanku to ya wanketa sau bakwai
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Idan kare ya sha a kwaryar ɗayanku to ya wanketa sau bakwai
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Idan kare ya sha a kwaryar ɗayanku to ya wanketa sau ba…
Bayanin hadisin: Idan kare ya sha a kwaryar ɗayanku to ya wanketa sau ba…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da wanke kwarya sau bakwai idan kare ya shigar da harshensa a cikinta, na farko daga cikinsu a haɗa da turbaya sai ruwa ya biyo bayanta, sai cikakkiyar tsafta ta tabbata daga najasarsa da kuma cutarsa.
Koyarwar hadisin: Idan kare ya sha a kwaryar ɗayanku to ya wanketa sau ba…
- Yawun kare najasa ne najasa mai kauri.
- Lallagin kare a cikin kwarya yana maida ita mai najasa, kuma yana najasantar da ruwan dake cikinta.
- Tsarkakewa da turbaya da maimaitawa sau bakwai ya kebanci tsarkakewa ne daga lallaginsa banda fitsarinsa da bayan gidansa, da ragowar abinda kare ya bata shi .
- Yadda wanke kwarya da turbaya: A sanya ruwa a cikin kwarya sai a zuba turbaya (kasa) a ciki, sannan a wanke kwarya da wannan cuɗaɗɗen.
- Zahirin Hadisin mai gamewa ne a dukkanin karnuka, har karnukan da shari’a ta bada iznin a dauke su, misalin karnukan farauta da na gadi da na kiwo.
- Sabulu da makilin ba sa tsayawa a matsayin turbaya; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nassanta turbaya ne.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· TSARKI
· FIƘHU DA USULU
· GUSAR DA NAJASA
· MAZUBAI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa